Duk mai son kawo ɓarna a Kannywood ya kama gabansa, don yanzu lokacin gyara ne, inji Abba El-Mustapha

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Sabon Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ya sha alwashin duk mai yiwuwa wajen kawo gyara da kyautata ɗabi’un jama’a a matsayin sa na shugaban hukumar iya tsawon lokacin da Allah ya ba shi dama zai yi a kujerar shugabancin nasa.

Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 24 ga Yuli, a lokacin da yake jawabi a gaban ɗumbun jama’a na cikin masana’antar Kannywood da kuma masoyansa da suka raka shi ofishinsa domin kama aiki.

Abba El-Mustapha ya fara da cewa, “Ni ɗan fim ne da ke taka rawa da dama a harkar, domin ina matsayin jarumi, kuma marubucin labari, furodusa, kuma wani lokacin na kan zama darakta, don haka akwai wani ciwo da ya ke damu na a zuciya ta tsawon lokacin wanda duk lokacin da na tuna abin ya kan yi mini ciwo a zuciya.”

Jarumin ya cigaba inda ya bayyana wa mahalarta taron wannan ciwo ko ince abi da ke ci masa tuwo a ƙwarya, wanda ya bayyana cewa, ba shi kaɗai ba, duk wani mai kishin masana’antar Kannywood yana da wanna ƙurjin.

Ya ci gaba da cewa, “Ba ni kadai ba duk wani mai kishin wannan masana’antar yana da wannan ciwon, kuma wannan ba wani ciwo ba ne sai irin yadda lamura suka lalace a wannan masana’antar ta hanyar rashin tsari.

“Don haka a wannan lokacin mun shirya mu yi gyara saboda haka duk wanda yake gudanar da wasu ayyuka da ba su da ba su dace ba, to idan har ba zai daina ba, to ya kama gabansa. Domin ba za mu bari a ci gaba da yin abubuwan da ba su dace ba. Mu masu kishin addininmu ne da yarenmu da kuma al’adunmu.” Inji shugaban.

Ya ƙara da cewa “Babban abin da na ke buƙata ga abokan aikina na wannan gida da kuma abokan sana’ata ‘yan fim shi ne, ina fatan ku ba ni haɗin kai da goyon baya tare da shawarwari masu inganci don ganin mun samu nasara wurin yin aikin da muka sa a gaba.

Kuma ina ƙara tabbatar muku da cewa, aiki muka zo ba wasa ba, duk wanda yake ganin zai kawo mana varna a wannan masana”antar to tun wuri ya kama gabansa.”

Daga ƙarshe ya yi wa ɗumbunjama’ar da suka yi masa rakiya godiya da fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *