Duk namijin ƙwarai ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba – Khadija S. Mohammed

DAGA AISHA ASAS

Wannan makon mun yi wa ma su karatun jaridarmu babban kamu a wannan shafin, domin mun samu damar tattaunawa da matar nan da ke bai wa ma’aurata da masu shirin yin aure shawarwari domin inganta zaman aurensu, har ta kai su kasance takalmin kaza. Da yake irin wannan cibiya ta Khadija Sa’ad Mohammed tamkar baƙon abu ne ga mutanen Arewacin Nijeriya, amma idan masu karatu suka biyo mu za su ji yadda baƙuwar tamu suke samun koke da jin matsalolin zamantakewar aure da kuma yadda suke bada shawara kuma a samu mafita da daidaito. Ga dai yadda tattaunar tasu da AISHA ASAS ta kasance:

Masu karatun mu za su so jin tarihin ki a taƙaice.
Suna na Khadija Sa’ad Mohammed. An haife ni a garin Kaduna, kuma ni ‘yar asalin garin Kaduna ce, cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa. Na yi makarantar nursery da firamare a ‘Raulatul Atfal Nursery & Primary School’, sai na tafi makarantar sakandaren ‘yan mata ta GGSS Tafawa Ɓalewa way, wanda a yanzu ta koma jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Bayan na kammala karatuna na sakandare sai na tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kaduna wato ‘College of Admininstration and Bussiness Studies (CAPS) Kaduna Polytechnic’ a inda na karanci harshen Turanci wato ‘English Language’. Daga nan kuma sai na koma makarantar horas da malamai ta ƙasa reshen Jihar Kaduna wato (National Teachers Institute NTI ), a inda na karanci ‘Guidance and Counselling’. Bayan na kammala sai na sake komawa Kaduna Polytechnic karo na biyu inda na karanci ‘Public Administration’. Bayan na kammala ne kuma sai na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria na karanta ‘Language Arts’. Yanzu haka kuma ina karatu a ‘Center for Muslim & Christians Studies Houston, Texas USA.

Na yi aikin koyarwa na tsawon shekara 11 a makarantu daban-daban, sannan daga nan na yi aiki da kamfanin ‘Dialogue Group of Companies’ da ke Kaduna tsawon shekara biyu, sannan na yi aiki da gidan talabijin na Liberty TV da ke Kaduna tsawon shekara 3. Sannan kuma ina sana’ar zane kala-kala wato ‘Art and craft’.
Ina da ƙungiya da ake yi wa laƙabi da ‘Babbar Mace Counselling Services’ wanda babban offishinmu yana kan titin Marnona a Unguwar Sarki Kaduna jikin ɗakin taro na masallacin Sultan Bello. Ƙungiya ce wacce ta ke maida hankali wajen saita tunanin ɗan-Adam domin rayuwarsa ta inganta, musamman mata.
An buɗe cibiyar ne a shekarar 2013 inda muka samu cikakkiyar rajista a shekarar 2015 a matsayin cibiya ta bada shawarwari game da damuwar al’umma. Sannan muna horas da ɗalibai masu shirin tafiya makarantun gaba da sakandare da kuma yaran da aka sama ranar aure.

A matsayin ki ta mace mai bai wa ma’aurata ko masu niyyar yin aure shawarwari, shin kina ganin ana samun daidaito da zaman lafiya ga ma’auratan da ku ke ba shawarar ko kuwa?
Tabbas ana samun nasarori, domin mata da yawa suna zuwa da niyyar fita daga gidajen mazajensu amma daga ƙarshe sai ka ji sun ɓuge da cewa “Kina ganin zai canza halayyarsa”? “Yanzu idan na yi abin da kika ce zai yafe min?” Da dai sauran su. To alhamdu lillah gaskiya mun gyara aurarraki da yawa, kuma mun inganta masu shirin rugujewa. kuma babban abin farin ciki shi ne, yadda al’umma suka fahimci muhimmancin zuwa neman shawara a wajenmu kafin su yanke hukuncin fita daga gidajen aurensu.

Ma’aurata suna zuwa miki da matsaloli iri daban-daban domin ki nuna musu hanyar vullewa, shin waɗanne irin matsaloli ne ma’aurata suka fi kawo kuka dangane da abinda ya shafi zaman aurensu?
Ma’aurata suna yawan kawo mana matsala game da mu’amalar auratayya, ma’ana saduwar aure, sannan matsalar tarbiyyar yaransu da batun abokiyar zama (kishiya).

Ya kike ganin zamantakewar auren macen da ba ta tsafta za ta kasance a gidan aurenta, shin zai iya kawo mata babban cikas tsakaninta da maigidanta?
Ya na daga matsalolin da ke sawa maza suna tsanar matansu, ai duk macen da ba ta da tsaftar jiki da ta muhallinta, to za ta samu babbar matsala da mijinta. Ba ma wannan kaɗai ba, domin rashin tsafta tana haifar da ƙwayoyin cuta waɗanda za su iya haddasa cututtuka daban-daban, ƙazanta babbar nakasu ne a wajen mace, musamman matar aure.

Tun lokacin da kuka fara wannan tafiya zuwa yanzu waɗanne irin nasarori kika samu?
Alhamdu lillah cikin manyan nasarorin da muka samu akwai wayewar kan da al’umma suka samu wajen fahimtar cewa idan kana da matsala a rayuwarka akwai wuri da aka tanada musamman domin a saurare ka, a ji damuwarka sannan a ba ka ingantattun shawarwari daga wajen ƙwararru a wannan ɓangaren, kamar yadda idan mutum ba shi da lafiya zai ɗauki ƙafarsa ya tafi asibiti ya yi wa likita bayanin damuwarsa. Sannan abu na biyu iyaye sun ba mu haɗin kai wajen kawo mana ‘ya’yansu a horas da su zamantakewar aure kafin a ɗaura musu auren, waɗanda za su tafi makarantar gaba da sakandare ma suna kawo su domin samun horo na musamman game da abinda ke tunkarar su. Matasa da suka samu kansu a cikin yanayi na ƙunci sakamakon yaudara ko cin amana a soyayya, suna kawo kansu da kansu domin neman shawarwari, wasu kuma sun fara shaye-shaye suna so su daina.

Qalubale fa?
Ƙalubalen da muka samu a baya shi ne, irin wannan cibiya ta bada shawarwari ta na ɗaya daga cikin na farko-farko a Arewacin Nijeriya, saboda haka mutane ba su saba da irin tsarinta ba, da aikace-aikacen da muke yi ba, sai da muka yi tsawon kusan shekara guda muna yin ‘seminars’, ‘lectures’, da ‘awareness campaign’ a kan muhimmancin cibiyar, kafin al’umma suka yadda suka karɓe mu hannu biyu, domin a baya wasu suna ganin kamar tonan asiri ne, ka zo ka faɗi damuwarka a wajen wanda ba ɗan’uwanka ba.

Kin taɓa cin karo da wata babbar matsala wadda ba za ki iya mantawa da ita ba da wata ta taɓa tunkarar ki ko wani domin ki bada shawara a kai?
Tabbas na taɓa cin karo da matsalar da ta dame ni a cikin wannan aiki, bisa al’adar aikinmu raba aure shi ne abu na ƙarshe da ba ma farin ciki da yin sa, domin mu aikinmu gyaran aure ne domin kar ya lalace. Akwai wata yarinya da ta kawo mana ƙarar mijinta, cewa yana yi wa kansa allurar ƙwaya, wanda har ya kai matakin da hannunsa ya fara ruɓewa saboda allurar da yake yi, sannan ba ya fita daga gida domin nemo musu abincin da za su ci, saboda yana gudun kar mutanen unguwa su gan shi, sai cikin dare ya ke fita domin ya sayo sabbin allurai kuma ya zubar da waɗanda ya riga ya gama amfani da su. Da muka bincika muka gane wannan al’amari tabbas gaskiya ne, babu yadda muka iya dole muka tura su kotu da takardar binciken da muka yi domin neman a raba wannan aure, kuma alhamdu lillah an samu nasara domin kotu ta raba wannan aure, sannan ta ba ita yarinyar ɗansu guda domin ta kula da tarbiyyarsa, sannan mijin aka bada takarda a kai shi asibitin duba masu matsalar ƙwaƙwalwa domin a kula da shi.

A ganin ki me ke kawo yawan rabuwar aure musamman a cikin al’ummar Hausawa?
Yawan sakin aure yana samuwa ne saboda dalilai kamar haka: Na ɗaya rashin sanin mene ne ma’anar aure, me ya sa zan yi aure, ko me ya sa na zaɓi wane/wance a matsayin abokin/abokiyar rayuwata?

Na biyu yin soyayyar son zuciya, ma’ana son mutum ƙwallin-ƙwal ba tare da son abubuwan da ya/ta ke so ba. Misali namiji ya na son mace ita kuma tana son kila ta yi karatu, ko kasuwanci ko wani buri nata na rayuwa, sai bayan sun yi aure sai ya zama ya fara nuna ƙiyayya ga duk wani abu da ita take so, ko kuma mace ta auri namiji domin tana son shi, bayan ta shiga gidan sai kuma ta fara nuna kishi ko ƙiyayya ga ‘ya’yansa ko matarsa ta gida, ko kuma idan ya ga wata ya ce yana so zai ƙara aurowa ta shiga ta fita sai ta hana wannan auren.

Sai na uku shi ne soyayya ba domin Allah ba, so na kwaɗayi saboda kuɗi ko muƙami. Na huɗu rashin iya mu’amalar auratayya (saduwar aure). Ko rashin ɗaukar aure a matsayin Ibada kuma hanyar shiga aljanna. Sai kuma rashin tattauna matsalolin zamantakewar aure a tsakanin ma’aurata.

Ya maganar iyali fa akwai su?
Na yi aure amma Allah bai ba ni haihuwa ba, amma akwai ƙanne da yaran ‘yan’uwa da na ke riƙewa.

Me ke saurin ɓata miki rai?
Gaskiya abinda ke saurin ɓata min rai shi ne a yi min ƙarya, idan na zo daga baya na gane gaskiyar lamarin abin yana sani takaici.

Wace kala ki ka fi so a rayuwarki?
Kalar sararin samaniya, wato ‘sky blue’.

Wane abinci ne bai saurin gundurar ki?
Tuwon shinkafa da miyar taushe.

Ko Hajiya Khadija na shiga harkokin siyasa ko tunanin riƙe wani matsayi a cikin ta?
Gaskiya a’a, ban taɓa shiga harkar siyasa ba, domin ina ganin ma kamar ba zan iya ba.

A wannan zamanin mata sun ɗauki kishi da zafi har ta kai wasu suna kashe kishiyoyinsu ko mazajen. Shin me za ki ce a kan hakan?
Gaskiya matan wannan zamanin sai addu’a, saboda sun bari kishi na jahilci da kishi na fita addini ya na ɗawainiya da su, sun bari zuciyoyinsu suke jan akalar rayuwarsu, mene ne amfanin ki kashe kishiyarki, ke kuma ki ƙare a gidan yari har ƙarshen rayuwarki, shi kuma mijin da ki ka yi faɗa domin shi ya auri wata? Duk namijin arziki ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba, mace an santa da tsoro, tausayi da yafiya, duk macen da ta sauka a wannan tsarin kuwa to ta zama mata-maza, kuma wallahi ba ki auruwa! Kishi shi ne ki baje basirar iliminki na soyayya domin karkato hankalin mijinki zuwa gare ki, me kishiya za ta tsare miki, ki yi harkarki ta yi nata, kowacce dai ta yi iya yin ta wajen kyautata wa maigida; miji ne kawai kuka haɗa, idan kuma ba ki iya jure zama da kishiya to ki fita gidan ki bar ma ta mijinta.

Me za ki ce game da auren dole da ake yi wa wasu yaran?
Gaskiya auren dole ba ya cikin tsari, a shari’ar musulunci ma ba a yarda da shi ba, amma alhamdu lillah kamar yanzu abun yanayin sauƙi, kasancewar malamai da ƙungiyoyi suna ta faɗakarwa game da hakan, yaran da aka yi wa auren dole ina ba ku haƙuri kuma ina ba ku shawara da ku yi haƙuri ku zauna ɗakunan aurenku, matuƙar ba a cutar da ku da komai. Saboda aure ya fi alkhairi sau dubu fiye da rayuwar zawarci. Saboda haka ne ma har na rubuta littafi mai suna ‘Babbar Mace Mai Aji’ domin mata su karanta su amfana; na yi shi ne cikin harshen Hausa da kuma na Turanci ‘The Noble Woman’. Littafin yana koya wa mata yadda za su zama masu cikakkiyar tarbiyya sannan su gane abubuwan da suka dace su rinƙa yi, da waɗanda bai dace su yi ba, da yadda za su koma manyan mata masu aji. Mata na sayen littattafanmu na amfani da kuɗin wajen zuwa makarantun gwamnati na ‘yan mata muna wayar musu da kai da yadda za su zama masu cikakkiyar tarbiyya da kuma sanin muhimmancin ilimi da kamun kai a matsayinsu na mata, sannan illolin shaye-shaye da karuwanci.

Wane buri ki ke da shi ko wane mataki ki ke da burin cimma wa a wannan ƙungiya ta ki?
Babban buri na yanzu in ga na buɗe rassan wannan cibiyar a dukkanin jihohin Arewacin Nijeriya, kasancewa al’ummarmu suna buƙatar irin waɗannan cibiyoyi domin samun shawarwari game da abubuwan da suke damun su.

A taƙaice wace shawara za ki ba ma’aurata don inganta zaman auren su?
Shawarata ga ma’aurata su yi zama da junan su bisa amana, kuma aure bautar Ubangiji ne, kuma hanyar shiga aljanna ce.

To mun gode ƙwarai da gaske.
Ni ke da godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *