“Ina jin takaicin tarin kura-kuran da ake yi a allunan talla”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Zubairu Balannaji ba boyayyen suna ba ne, musamman a tsakanin marubuta na Jihar Kano, inda yake rayuwa kuma yake baje irin tasa basirar da Allah Ya ba shi ta ƙirƙirar labari, da fitar da labarin da aka sawwala shi daga tunani zuwa ga rayuwa, ma’ana dai ya mayar da shi zuwa fim. Matashin marubucin littattafan adabi, marubucin wasan kwaikwayo, mai shiryawa da tsara finafinan Hausa, kuma a gefe guda ɗan kasuwa. A tattaunawar sa da ABBA ABUBAKAR YAKUBU fasihin marubucin ya bayyana irin gwagwarmayar da ya taso a cikin tun daga marubuci mai tatata har ya kai ga matakin da yanzu tauraronsa ne ke haskawa a tsakanin marubutan finafinan Hausa masu dogon zango da suke fice a yanzu. Na san ba za ku kasa kallon fim ɗin ‘Kan Ta Ƙile’ ba, wanda ya fito daga ƙoramar ilimin wannan baƙon marubuci namu na yau. A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Mu fara da gabatar da kanka.
BALANNAJI:Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu. Da farko dai sunana Zubairu Musa Balannaji, wanda a ka fi sani da Zubairu M. Balannaji. Ni marubuci ne, manazarci, sannan kuma mai tsarawa da shirya finafinai. Har wa yau kuma ni ɗan kasuwa ne da ke harkar sayar da labulayen ado na zamani da zannuwan gado, na gida da ƙasashen waje, da sauran kayan ƙawata gida, da duk dai wani abu da ya shafi ƙawata cikin gida (interior decoration). Ina kuma yin aikin ƙawata wajen biki da sauran tarurruka (Decorations).
Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
To, ni dai asalin Bakano ne gaba da baya. An haife ni a garin Kano, kuma na tashi a Kano. Na yi karatuna tun daga makarantar rainon yara (Nursery) har zuwa matakin sakandire a makarantar ma’aikatan Kwalejin Ilimi ta F.C.E da ke nan Kano, wato daga Fedwa Nursery International School, zuwa Demonstration Primary School, na kammala a F.C.E Staff Secondary School.
Bayan na kammala sakandire sai na ƙara komawa asalin ita F.C.E ɗin dai inda na yi karatun koyon ilimin malanta wato N.C.E, inda na ƙaranci fannin harshen turanci da Hausa, na kuma kammala a shekarar 2015. Yanzu haka ina nan zaune a Kano ina ci gaba da sauran harkokina na rayuwar rubuce-rubuce, shirya finafinai da kuma sauran kasuwanci da na ke gudanarwa, kamar yadda na ambata a baya. Batun iyali kuma ina kan hanya, nan ba da jimawa ba za a ga katin ɗaurin aurena, saboda na samu matar aure har ma mun gama daidaitawa da ita. Saboda haka zan yi amfani ma da wannan gavar na roƙi addu’o’i daga masoyana, a kan Allah Ya tabbatar mana da dukkanin alkhairan da ke tattare da wannan aure da mu ka ɗaura aniyar yi, Ya kuma tsare mu daga dukkanin abin ƙi.
Menene Balannaji ke nufi?
Balannaji dai suna ne na zuriyar gidanmu. Ainihin sunan kakana ne wanda ya haifi mahaifina, wanda ake kira da Bala, to ya taso a hannun kakarsa mai suna Naji, saboda yadda ta ke matuƙar ji da shi sai a ke kiransa da Balannaji, ma’ana dai Bala na Naji. To, daga haka ne kuma sunan ya bi shi har zuwa girman sa.
Ba ni labarin yadda aka yi ka fara sha’awar rubuce rubucen adabi?
Na fara ne da sha’awar karance-karance tun ina aji ɗaya na firamare. To, daga baya kuma lokacin ina aji 3 na firamare ɗin sai na fara sha’awar ni ma na bayar da ta wa gudunmawar a fannin rubutu, tun daga nan na fara jagwalgwalawa. Idan na rubuta a wancan lokacin sai na bai wa abokaina su riƙa karantawa, wanda a farko ma ba su yarda cewa ni ne nake rubutawa ba, har dai daga baya da suka ga wataran ina zama na rubuta a gabansu sannan suka saduda suka yarda cewa ni ne nake rubutawa da kaina.
To, idan na ba su littattafan su karanta bayan na kammala rubutawa a haka wasu za su yage, saboda karva-karɓar da a ke yi a tsakaninsu, wasu ma su ɓata. To, amma dai ban samu damar wallafa littafin ya shiga kasuwa ba, sai a 2006 da na rubuta littafin Zakaran Da Allah Ya Nufa… Na bayar da aikinsa, wanda bai samu shiga kasuwa ba sai a farkon shekarar 2008.
Wanene jagoranka na farko da ya fara ba ka shawarwari ko taimako kan harkar rubutun adabi?
Gaskiya jagorana ta farko ita ce mahaifiyata, sai kuma ƙannaina, da kuma yayata Hajiya Bilkisu M. Sani Balare. Waɗannan mutanen da na zayyano maka su ne farkon waɗanda na ke zaunawa da su idan na samo wani sabon tunani kan labari su baba ni shawarwari har na kai ga nasarar gina labarin kafin na kai ga fara rubutawa, musamman ma dai mahaifiyata.
Ka rubuta littattafai guda nawa? Ba mu labarin wasu daga ciki, wanne labari suka ƙunsa?
Zuwa yanzu dai na wallafa littafai 22 ne waɗanda suka shiga kasuwa, sai kuma wanda nake kan aikinsa, shi ne na 23 mai suna An Bar Kari… wanda shi ma zai shiga kasuwa a bayan Sallah in sha Allahu.
Labari littafin ‘Auren Gayya’, labari ne da yake nuna illar son zuciya da kuma bin jama’a da mugun nufi, wanda a ƙarshe komai mugun abin da mutum ya shirya a farko to, fa zai dawo masa ne da tarin munanan sakamako a lokacin da bai zata ba bai tsammata ba. A cikin littafin na shirya labarin a kan wasu taurari wato Rumaisa’u da Asiya, wanda Asiya ita ce uwargida, daga baya kuma a ka auro mata Rumaisa’u a matsayin kishiya.
Ita Asiya tana zaune da Rumaisa’u da zuciya ɗaya, yayin da ita kuma ta shigo da mugun nufin fitar da ita daga gidan mijin ko ta halin ƙaƙa. Ta yi ta bin ta da sharri kala-kala, wanda a ƙarshe dai ta yi nasarar fitar da ita ɗin. Kwatsam! Kuma bayan ta kammala iddar ta sai ta haɗu da mahaifin Rumaisa’u suka ƙulla soyayya, a ƙarshe dai sai da ta yi nasarar aurensa.
Sai kuma littafin ƙarshen Butulu. Shi labari a kan wani malamin addini mai tsanani, wanda ko kaɗan ba ya duban kowanne irin cigaba da ya zo ta fuskar zamani, yana kallon duk wani abu da Turawa suka kawo na cigaba wanda a da can ba mu da shi a matsayin yahudanci. A na nan kwatsam! Sai wani Likita ya zo neman auren ‘yar sa.
Sai da soyayyarsu ta fara yin nisa sai ya sanya a yi masa bincike a kansa, inda su kuma waɗanda ya sanya su yi masa bincike suka binciko masa munanan dalilan da shi a wajensa ya ke ganin cewa sam ɗiyarsa ba ta dace da auren Bayahude irin Likita ba, saboda a binciken da aka yo an tabbatar masa cewa har aikin Gwamnati mahaifiyar saurayin ýar ta sa ta ke zuwa, wanda shi kuma ya ke kallon hakan a matsayin kafirci.
A ƙarshe dai ya tarwatsa ingantacciyar soyayyar da masoyan suka ƙulla ya aura mata ɗaya daga cikin almajiransa, wanda a zahirance yake a matsayin mutumin kirki, amma a baɗini yana da wasu mugayen halayen da kwata-kwata ma bai cancanci a ba shi aure ba. Bayan auren na su ne a hankali mugayen halayensa da ya keɓoyewa jama’a suka dinga fitowa.
Daga ƙarshe dai ya yi musu babban butulcin da su ka gwammace dama ɗan bokon suka bai wa auren ba shi ba. Sai kuma littafin da na ke kan aikinsa yanzu haka wanda ban taɓa rubuta irin shi ba ta fuskar ma’ana, mai suna An Bar Kari…
Wanne abu ne za ka iya ce wa shi ne tushen fara samun nasarar ka a matsayin marubuci?
Haƙuri da jajircewa tare da jiran lokacina ya zo ba tare da na yi gaggawa ba. Waɗannan su ne tushen samuwar dukkanin nasarar da na yi a duniyar rubutu.
Yaya aka yi ka samu kanka a matsayin marubucin finafinan Hausa?
Yadda na samu kaina a matsayin marubucin finafinan Hausa shi ne, dama can ina sha’awar harkar tun bayan fara fitar da littafina kasuwa, a lokacin na shiga ƙungiyoyin marubuta. A lokacin duk wata bita da za a shirya wa marubuta a kan sanin ƙa’idojin rubutu ko kuma koyar da rubutun fim da sauran duk wata bita da za a ƙaru da ilmi to, ba na tava bari ta wuce ni ba tare da na halarta ba.
Ta haka ne na koyi rubutun wasan kwaikwayo na fim. To, watarana kuma ina zaune a gida bayan na fitar da littafina mai suna ƙarshen Butulu, sai a ka kira ni a waya da baƙuwar lamba. Bayan mun gaisa sai ya gabatar min da kansa a matsayin Darakta kuma mai shirya finafinan Hausa, Aminu I. Tahir.
Ya ce min ya karanta littafina ne mai suna ƙarshen Butulu, kuma labarin ya ƙayatar da shi, yana so mu haɗu da shi mu tattauna na sayar masa da labarin zai mayar da shi fim. Na ce masa to, babu damuwa. Bayan mun haɗu mun tattauna ya sayi labarin ya mayar da shi fim a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011.
Waɗanne finafinai ka rubuta ko ka shirya kawo yanzu?
Na rubuta finafinai irin su ‘Ƙarshen Butulu’, ‘Gandara’, ‘Buje’, ‘Bayan Badala’, ‘Sakayya’, ‘Alƙawarin Zuciya’, ‘A Sanadin So’, ‘Zafin Kishi’, ‘Wasiyya’, ‘Nadiya’, ‘Maimuna Ganɗama’, ‘Auren Gayya’ (Series), ‘Kan Ta Ƙile’ (Series) da sauransu. Sai kuma wanda na shirya, ko kuma nake kan shirya wa tunda series ne, wato mai dogon zango ne guda ɗaya, kuma shi ne fim na farko da na fara shiryawa, wato ‘Kan Ta Ƙile’, wanda mun riga mun saki season 1, yanzu haka kuma muna kan aikin season 2 da 3 ne, shi ma mun kusa fara sakinsa very soon, Insha Allahu.
Ba mu labarin fim ɗin nan mai dogon zango, ‘Kan Ta Ƙile’, wacce rawar ka ke takawa a ciki?
Cikin ƙayataccen shirinmu mai dogon zango na ‘Kan Ta ƙile’ ina ta ka rawa ne a matsayin Producer, sannan kuma Marubucin da ya samar da baki ɗayan labarin shirin. Na kuma rubuta zango na farko na shirin, wato zango na farko. A yanzu kuma da muna tsaka da aikin zango na 2 da na 3 na shirin, ina taka rawar Maishiryawa wato Producer, sannan kuma wanda ya samar da gundarin labarin, bayan haka kuma ina ɗaya daga cikin marubuta 6 da ke zaman tsara labarin da rubuta shi.
Wanne ƙalubale marubuta labarai ke fuskanta a harkar shirya finafinai?
Ƙalubalen ba wasu masu yawa ba ne, da suka wuce kafin ka karɓu a wajen furodusoshi, su gane inganci da kuma ƙwarewarka a fagen rubutu. Amma da zarar sun gano ka ƙware to, fa ayyuka ma sai ka rasa yadda za ka yi da su, saboda za a yi ta kawo maka ayyukan ne daga ko’ina na cikin masana’antar. Sai kuma cinyewa marubuta kuɗi ko kuma kasa biyansu haƙƙoƙin aikinsu yadda ya dace. Amma game da wannan matsalar ta biyu idan har marubuci ya yi wa kansa kyakkyawan tsari to, zai kuɓuta daga zaluncin kowanne Furodusa.
Yaya ka ke kallon bambanci a rayuwarka, a matsayinka na marubucin littattafai da kuma marubucin finafinai? Wanne aka fi samu cigaba?
Gaskiya a yanzu dai kam fannin rubutun littafi sai dai shukuran kawai. Amma dai a shekarun baya kam Alhamdulillahi, mun mori harkar rubutu yadda ya kamata, kuma kusan ta kowacce fuska. A yanzu kasuwar littafin ta riga da ta mutu murus, don haka duk wanda ka ga ya buga littafi a wannan runtsin to, ba ƙaramin jarumi ba ne da ya kamata a jinjina masa, saboda ba don kuɗi a yanzu marubuci zai buga littafi ba, sai domin masoyansa da su ka saba da karatun littattafansa, har suke kewar rubutunsa, tare da nuna shauƙi a duk lokacin da suka ji zai buga sabon aiki, da kuma kishin Adabin Hausa.
Shi kuma ɓangaren rubutun fim babu laifi, saboda har gobe idan dai har ka ɗauke shi da muhimmanci kuma ka riƙe shi a matsayin sana’a to, za ka ci gaba da cin gajiyar sa, don ko babu komai za ka ci abinci da shi, ka yi sauran buqatun rayuwarka, har ma ka taimaki na kusa da kai. Don haka in dai maganar cigaba a ke yi to, fannin rubutun fim ya fi ci gaba. Amma ni daga ɓangarena har kwanan gobe na fi ƙaunar rubutun littafi, kuma ko da littafin da na rubuta ma na fi ƙaunarsa fiye da fim ɗin da na rubuta.
Menene ka ke ganin zai bai wa marubuta tasiri da ƙarfin faɗa a ji a harkar shirya finafinai?
Idan har marubuta muka ɗauki rubutun da muke yi da muhimmanci, muka kuma ƙara inganta rubutun namu, tare da faɗaɗa bincike a kan dukkanin wani abu da za mu rubuta, sannan kuma muka haɗa kawunanmu to, ba a harkar shirya finafinai ba, ko da a Majalisar Ɗinkin Duniya ne za mu iya zamowa daga gaba-gaba, kuma masu faɗa a ji. Amma idan har muka aikata saɓanin haka, muka kuma cigaba da tafiya a yadda muke a yanzu, to tabbas babu inda za mu je a ji amonmu yadda ya kamata.
Wanne abu ne ya faru da rayuwarka a matsayinka na marubuci, wanda ba za ka manta da shi ba?
Gaskiya abubuwan da suka faru da ni a matsayina na marubuci suna da yawa, masu daɗi da marasa daɗi. Shekaru kusan goma sha bakwai ana abu ɗaya ai dole za a ci karo da abubuwa da yawa. Amma Alhamdulillahi arziƙin jama’a da kuma alfarmar shiga muhimman wurare, tare da mu’amala da muhimman mutanen da in ba don sanadin rubutu ko fim ɗin ba shi ne abin da na fi duba a matsayin muhimmai.
Wacce shawara za ka bai wa matasan marubuta da ke sha’awar fara rubutun fim?
To, shawarar da zan bai wa matasan marubuta masu sha’awar fara rubutun fim ita ce, a ko da yaushe su kasance suna duban abinda za su rubuta da kyakkyawar fuska, ta hanyar duba addini da al’adunmu fiye da komai, hakan ne zai ba su damar yin rubutu mai inganci, sannan su kasance masu bincike a kan dukkanin abinda za su rubuta. Su sani dukkanin abinda suka rubuta abin tambaya ne a gare su ranar gobe ƙiyama.
Su fifita addini da kyawawan al’adunmu fiye da kuɗin da za su samu, wanda za su iya ƙarewa a kowanne lokaci su bar su da tarin zunubi idan har ba su yi taka-tsan-tsan da abinda za su rubuta ba. Alƙalami yana da santsi da yawa. Ya kamata kowanne Marubuci ya dinga neman tsari daga santsinsa a kullum a kuma koda yaushe.
Ta wacce hanya ka ke ganin za a inganta dangantaka tsakanin marubuta, masu shirya finafinai da ɓangaren gwamnati?
To, ai dama tuntuni ya kamata a cemarubuta suna cikin gwamnati, saboda tasiri da muhimmancinsu a cikin al’umma. Amma saboda mu marubuta ba mu da yawan kutse-kutse irin na ‘yan fim shi ya sa ba a tafiya da mu a gwamnatance. Zuwa yanzu shawarar da zan bai wa ‘yan’uwa marubuta baki ɗaya ita ce, ya kamata mu ma mu kutsa kanmu cikin gwamnatin ba wai mu dinga tsayawa jiran sai an neme mu ba.
Abin takaici sai ka ga ƙungiyoyin masu ƙananan sana’o’i da ba su kai na marubuta muhimmanci da tasiri a cikin al’umma ba za ka ga sun shiga cikin gwamnati sun yi kane-kane ana damawa da su, amma mu marubuta mun mayar da kanmu koma baya. Sannan ina kira ga gwamnati da ta dubi marubuta da idanun basira, ta jawo mu a jiki domin mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da ƙasar da harshenmu da ma kyawawan al’adunmu gaba a idon duniya.
Ina jin matuƙar takaici idan ina kallon allunan talla a bakunan titi, saboda tarin kura-kuran da ake samu a cikin mafi yawansu da kuma gurɓatacciyar Hausa wadda sam! Za ta yi wa mutane wuyar fahimta bare har su iya fassara abinda a ke nufi. Ya kamata a ce duk wani talla da za a yi ya zagaya duniya to, ya kasance wasu daga cikin gogaggun marubuta ne suka tsara shi suka rubuta shi, saboda su sun san ƙa’idojin rubutu da kuma alamomin rubutu. Bugu da ƙari kuma marubuta suna da salo da sarrafa harshe da kuma balagar zance.
Bangon littafin ‘Auren Gayya’
Sai batun marubuta da masu shirya finafinai, wanda shi a yanzu an ɗauko muhimmiyar gavar gyara. Saboda a yanzu furodusoshi sun gane muhimmancin marubuta, sun kuma yarda cewa duk wani kyakkyawan labari zarensa ba ya kammala ƙulluwa ya bayar da ma’anar da ta dace da shi har sai ya kasance cewa marubuta ne suka rubuta gami da tsara shi, musamman ma gogaggun marubuta irin na littafi. Savanin a baya da suke kallon marubuta tamkar mayunwata ko kuma bayin su.
Menene burinka nan gaba a wannan harka da ka ke yi?
Alhamdulillahi. dukkanin burikana a wannan harka sun cika, babban burina yanzu bai wuce gamawa da harkar lafiya, tare kuma da cikawa da imani na gama da duniya lafiya. Sai kuma na ƙarshe shi ne na ga al’umma ta ci gaba da amfana da rubututtuka da kuma finafinan da zan shirya a nan gaba, su ci gaba da kuma da fahimtar dukkanin saƙonnin da nake aika masu a rubutun littafi da kuma finafinanmu.
Wanne abu ne yake faranta maka rai da rayuwar marubuta?
Zumuncinsu da kuma karamcinsu, ta yadda za ka ga duk sha’anin wanda ya tashi a tsakaninmu na jaje ne ko na farin ciki za ka tarar da marubuta a sahun gaba mun yi dandazo don nuna lallai shi mai sha’anin namu ne. Ko da akwai masu saɓani tsakanin wasu da mai sha’anin za ka tarar an kau da komai na matsala an fuskanci abinda ya kamata.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?
Sana’a goma maganin mai gasa. Shi ya sa ma na ke da sana’o’i da yawa (dariya).
Na gode.
Ni ne da godiya. Masha Allah.