Duk wanda ya sauya sheƙa a bakin kujerarsa, garaɗin APC ga sanatocinta

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyya mai mulki ta APC ta gargaɗi sanatocinta masu shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar PDP cewa, suna iya rasa kujerunsu muddin suka aikata hakan.

APC ta yi wannan barazana ne bisa la’akari da shirin da wasu sanatocinta su 15 ke da shi na ficewa daga jama’iyyar.

Jam’iyyar ta faɗa wa sanatocin cewa, ficewa daga cikinta kasada ce babba domin kuwa hakan ka iya zama sanadiyyar rasa kujerunsu a Majalisar Tarayya.

A hannu guda, su ma sanatocin kansu cike suke da tsoron kada bayan sun sauya sheƙar PDP ta ƙi cika alƙawarin kyautata musu da ta yi, musamman ma ganin cewa babu garantin jam’iyyar mayyar za ta iya kai bantenta a zaɓen 2023.

Haka nan, ba lalle ba ne sanatocin su cim ma ƙudirinsu ko da kuwa sun koma PDP, domin ita PDPn ta riga ta faɗa musu cewa ba za ta iya sauya sunayen ‘yan takararta da ta miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙaza (INEC) ba.

A hannu guda, ƙungiyar ƙabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, ta nuna cewa duk wata jam’iyya da ta hana shiyyar Kudu maso Gabas tikitin takarara Shugaban Ƙasa, ba za ta shaƙi ƙamshin nasara ba balle kuma ta same ta a shiyyar.

Majiyoyin jaridar The Nation sun ce, sanatocin APC da suka kasa samun tikitin sake tsayawa takarar na nazarin yiwuwar ficewa daga jam’iyyar zuwa wata don cim ma burinsu.

An ce sanatocin da lamarin ya shafa sun ɗora laifin haka a kan gwamnonin jihohinsu na gaza samun tikitin sake tsyawa takara da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *