Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya gargaɗi ’yan siyasa daga Arewa da ke shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 da su haƙura, yana mai cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas. Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin shugabanni da mambobin PBAT Media Centre da Tinubu Northern Youth Forum (TNYF) a sakatariyar APC da ke Abuja.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da bin tsarin rabon mulki tsakanin kudu da arewa, yana mai tunatar da cewa bayan shugabancin shekaru takwas na wani daga Arewa, jam’iyyar ta tabbatar shugaba daga kudu ne ya gaje shi. Ya ce: “Mun dage cewa shugabancin ƙasa ya koma kudu bayan shekaru takwas na shugabanci daga Arewa, kuma yanzu da hakan ta tabbata, Tinubu zai sake tsayawa a 2027. Bayan haka ne mulki zai koma Arewa.”
Ganduje ya bayyana cewa, ko da yake akwai matsaloli a ƙasar, manufofin Tinubu na kawo sauyi sun fara yin tasiri, musamman a ɓangaren tattalin arziki. Ya kuma yaba wa matasan Arewa da ke goyon bayan mulkin Tinubu, inda ya ce irin goyon bayan da suke bayarwa zai taimaka wajen ci gaban Najeriya. A nasa ɓangaren, shugaban Tinubu Northern Youth Forum, Malam Auwal Ibrahim, ya tabbatar da cewa kungiyar su na da shirin samar da ƙuri’u miliyan biyar domin sake tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2027.