Duniya na fuskantar barazanar ƙarancin ruwa – MƊD

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa duniya na cikin barazanar fuskantar ƙarancin ruwan sha saboda amfani da buƙatar ruwa sosai da ake da ita ga kuma matsalar sauyin yanayi.

“Duniya na cikin matsalar faɗa wa mawuyacin hali saboda yawan amfani da ruwa,” inji rahoton.

Wallafa rahoton na zuwa ne gabanin taron MƊD na farko kan ruwa tun 1977.

Dubban wakilai ne daga sassan duniya za su halarci taron ƙolin na kwanaki uku da za a yi a birnin New York daga ranar Laraba.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce yanayin da ake amfani da ruwa a yanzu ba mai ɗorewa ba ne, kuma wannan yanayin tamkar jinin bil Adama ne ke tsiyayewa saboda matsalolin ƙarancin ruwan da ɗumamar yanayi da gurɓatar muhalli ke ci gaba da haifarwa.

Babban editan da ya wallafa rahoton da aka kira da World Water Development Report wanda MƊD ta ƙaddamar, Richard Connor ya ce duniya na fuskantar gagarumar matsala.

“A halin yanzu, kashi 10 cikin 100 na al’umomin duniya na rayuwa ne a ƙarƙashin wani yanayi na matsanancin ƙarancin ruwa. A cikin rahotonmu, mun ce kimanin mutum biliyan uku da miliyan 500 na rayuwa ne a ƙarƙashin rashin wadataccen ruwa na tsawon wata guda aƙalla cikin kowacce shekara.”

Mista Connor ya faɗa wa manema labarai cewa ana ci gaba da samun matsala waje samar da ruwan sha a faɗin duniya.

“Idan ba mu shawo kan matslar ba, zai iya zamantowa barazana a duniya,” inji shi.

Jami’ar MƊD wadda za ta karɓi baƙuncin taron kan batun ruwa, Usha Rao Monari, ta faɗa wa BBC cewa ya kamata a san yadda ake kula da kuɗaɗe da aka tanadar na samar da ruwan sha a nan gaba.

“Akwai ruwa mai yawa a doron duniya, idan muka san yadda za mu kula da shi, to za mu iya zama tare da ruwa na gwamman shekaru masu zuwa,” inji Monari.

“Ina ganin ya kamata gwamnatoci su samu sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe, da sabbin hanyoyi na amfani da ruwan sha. Ina ganin fasaha da kuma ƙirƙire-ƙirƙire za su taimaka wajen ganin yadda za a kula da ɓangaren ruwa da kuma amfani da shi.”

Taron wanda gwamnatocin Tajikistan da Netherlands za su karɓi baƙunci, zai tara mahalarta 6, 500, wanda ya ƙunshi ministoci 100 da kuma shugabannin gwamnatocin duniya daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *