Duniya na matuƙar buƙatar haɗin kai sama da ko wane lokaci a tarihi

Daga CMG HAUSA

Sanin kowa ne cewa, a yanzu haka duniyar bil adama na fuskantar manyan ƙalubale, da matsaloli a matakai daban-daban, wasu na ƙasa da ƙasa, wasu kuma na shiyyoyi.

Matsalolin ci gaba da yaɗuwar annobar COVID-19, da rikicin Ukraine, da ƙamfar cimaka, da yaɗuwar fatara, da ƙalubalen sauyin yanayi, kaɗan ne daga cikinsu.

Hakan ne ma ya sa a cikin jabawin da ya gabatar yayin buɗe babban taron MƊD na 77, babban magatakardar MƊD Antonio Guterres ya tabo batun buƙatar da ake da ita, ta hada ƙarfi da ƙarfe wajen shawo kan matsalolin duniya.

Mr. Guterres ya nuna damuwa, game da yadda duniya ke ƙara fuskantar ɓaraka, da watsi da tattaunawa, ko aiwatar da matakan warware matsaloli cikin haɗin gwiwa.

Har ma yake cewa, a baya-bayan nan, duniya na tunkarar yanayi na rashin haɗin gwiwa kwata-kwata, daga ɗan haɗin kai ƙalilan da a baya ake da shi.

Ko shakka babu wannan batu haka yake, duba da yadda ake ta samun rarrabuwar kawuna masu haifar da tashe-tashen hankula, a sassa daban-daban na duniya.

Wasu sassa suna kafa ƙawance domin muzgunawa wasu, suna watsi da dokokin ƙasa da ƙasa, wanda hakan tamkar yin watsi da dimokaradiyya ne, da ma sauran matakai na inganta haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

A lokutan da suka shuɗe da ma a yanzu, tarihi ya nuna buƙatar da dan Adam ke da ita ta haɗa kai da juna, a matsayin hanya daya tilo ta wanzar da ci gaba.

Don haka a yanzu ma, lokaci ne da ya kamata shugabannin duniya su rungumi haɗin kai, da “hada karfi da karfi” wajen shawo kan ƙalubalen dake addabar duniya baki ɗaya.

Masana dai sun sha bayyana cewa, ba wani ɓangare, ko ƙasa mai karfi ɗaya tilo, wadda za ta ita warware matsalolin ta, ko waɗanda suke addabar duniya baki ɗaya ita kaɗai.

Hakan na nufin idan har ana son kaiwa ga warware ƙalubalen da duniya ke ciki a yanzu da ma nan gaba, ya zama dole a komawa haɗin gwiwa da zaman jituwa.

Mai fassara: Saminu Hassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *