Duniya za ta more manyan damammaki uku daga ƙasar Sin mai buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje

Daga CMG HAUSA

A daren ranar Jumma’a 4 ga wata ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ta kafar bidiyo, ya halarci bikin ƙaddamar da baje-kolin kayayyakin ƙasa da ƙasa da ake shigowa da su ƙasar Sin ko kuma CIIE karo na biyar wanda ake yi a birnin Shanghai, inda ya yi jawabin dake jaddada cewa, ƙasarsa za ta taimakawa ƙasa da ƙasa, more damammakin ci gaba tare.

Xi ya ce, “Ya dace mu kara buɗe kofarmu, don daidaita matsalolin ci gaba, da faɗaɗa haɗin-gwiwa, da ƙara ƙarfin yin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma samar da ci gaba tare, ta yadda za’a ƙara dunƙule tattalin arzikin duniya baki ɗaya, da samar da ci gaba ga ƙasa da ƙasa, don kara amfanar al’ummominsu cikin adalci”.

A shekaru biyar da suka wuce, shugaba Xi ya sanar da gudanar da bikin CIIE, da zummar faɗaɗa buɗe kofar ƙasar Sin, ta yadda babbar kasuwar ƙasar za ta zama babban zarafi ga duk duniya baki daya.

Ƙididdigar ta nuna cewa, a wajen bukukuwan CIIE huɗu da suka gabata, adadin kayayyakin da aka baje ƙolinsu, sun kai dubu 270, kuma jimillar darajar yarjeniyoyin da aka daddale ta zarce dala biliyan 270, inda aka ɓullo da sabbin hajoji, da fasahohi, da hidimomi da yawansu ya wuce 1500.

Bikin CIIE, tamkar dandali ne ga ƙasar Sin, na kafa sabon tsarin samar da ci gaba, da faɗaɗa buɗe ƙofarta ga ƙasashen ƙetare, inda sassan ƙasa da ƙasa za su ci gajiya tare.

Baje kolin CIIE na bana, ƙasaitaccen bikin ƙasa da ƙasa ne na farko da ƙasar Sin ta gudanar, tun bayan da ta kira babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis karo na 20, wanda ya samu halartar ƙasashe da yankuna, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 145, gami da kamfanoni 284 dake sahun gaba a duniya.

Rahoton babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis karo na 20 ya jaddada cewa, ƙasar Sin za ta nace ga bin manufar buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje, tare da cin moriya tare da ƙasashe daban-daban, ta yadda duniya za ta amfani sabon ci gaban ƙasar Sin.

A jawabin shugaba Xi, ya sake nanata cewa, kasarsa za ta taimakawa ƙasashe da ɓangarori daban-daban, ta yadda za su more damamakin da suka shafi babbar kasuwar ƙasar, da manufar buɗe ƙofa ga ƙasashen waje, da habaka haɗin-gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa.

Manazarta na ganin cewa, damammakin uku, za su sanya babban kuzari ga tattalin arzikin duniya, wanda a yanzu haka yake murmurewa daga mawuyacin hali.

Mai fassara: Murtala Zhang