Duniyar Ƙirifto Karansi: Yaushe pi za ta fashe ne? (2)

Daga DANLADI Z. HARUNA

Tun a farkon shekara ta 2020 ake ta hasashen za a soma aiki da Pi a matsayin kuɗin intanet, wannan ta sa wasu ɗaliban Malam Nikolas musamman na ƙasashen Asiya, suka yi awon gaba suke ta buɗe kantuna da sunan ‘Pi Mall’, inda aka ce suna saye da sayarwa ta amfani da kuɗin Pi.

Da alama wannan abu yayi wa malamin daɗi, don haka ya ja wasu da dama cikin tsarin ta hanyar da ake kira ‘Hackathon’.

Sai dai ƙila hakan bai yi wa ɗaya daga waɗanda suka soma aikin daɗi ba. A watan Fabrairu na 2021, Dakta Vincent McPhillip ya sanar da janye hannunsa daga tafiyar, a dai-dai lokacin kuwa ana cewa saura wata ɗaya Pi ɗin ya zama kadara.

An tambaye shi dalilin haka, ya ce ba zai ce uffan ba saboda maganar na gaban kotu. Babu jimawa sai aka ji ya buɗe nasa tsarin mai suna Knomad. Kodayake, ya bayyana cewar, tun 2018 yake fafutukar samar da shi.

Ƙila wannan mahangurvar ta jawo wa Pi salalan tsiya, domin kuwa a da suna cewar sai an kai mutane miliyan goma kafin ta soma fashewa ana kwasar romo. Sai dai a lokacin mutane sun haura miliyan 15.

Ya zuwa yanzu kuwa an haura miliyan 35 amma shiru maƙatau. Su kansu ɗaliban da suke ta azarɓaɓin buɗe shagunan Pi, sun ga abin ba na ƙarau ba ne. Don haka, wani babban shagon Pi na gwaji mai suna PiChain ya sanar da daina aiki a cikin watan Oktoba na 2021.

Duk da haka, mutane sun ci gaba da buɗe shaguna a yanar gizo da wallafa hotuna da riguna da suke nuna cewar shi fa wannan abu mai suna Pi Network zahiri ne, kuma zai kawo mawalati fiye da tsammani.

Suna aiwatar da wannan abu ne a ƙarƙashin wata fasaha da masu abin suka kira Mainnet tare da Telnet waɗanda a nan ake ƙyanƙyashe sabuwar fasahar da za ta ƙara yayata Pi Network a Duniya.

To abin tambaya, me masana suke cewa, a yanzu dangane da Pi Network? Joel Agbo a shafin CoinGecko na ganin cewa Pi Network bai wuce matsayin kafar tattara jama’a domin samun kuɗin shiga daga tallace-tallace ba.

Ta yiwu Malam Agbo ya lamunta da ra’ayin Farfesa Karol Jenszura ne wanda yake ganin kurum wayo ne da dabara domin samun kuɗi ta intanet ga waɗanda suka ƙirƙiro abin. Ya ƙara da cewa, “Har abada Pi ba zai taɓa zama kuɗi ko wata kadara ba illa zunzurutun ƙarya da ɓata lokaci.”

A kan haka wani masanin harkar Kirifto Karansi, Mista Cem Dilmegani ya lissafo wasu al’amura da yake ganin Pi Network shifcin gizo ne. Babu wani abu da za a samu daga gare shi illa ɓata lokaci. Wasu daga hujjojin nasa su ne;

Za mu ɗora a rubutu na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *