Duniyar da babu zaman lafiya na buƙatar sake fuskantar hanyoyin zaman tare tsakanin ƙasa da ƙasa

Daga CMG HAUSA

A ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2013 ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a cibiyar hulɗar ƙasa da kasa ta Moscow, mai taken “Tsarin zamani, da inganta zaman lafiya da ci gaban duniya”, inda ya bayyana cewa, “ya kamata dukkan ƙasashen duniya su haɗa kai don ɓullo da wani sabon nau’in alaƙar ƙasa da ƙasa, wanda ke mayar da hankali kan samun nasara tare ta hanyar haɗin gwiwa.”

Wannan dai ita ce ziyarar farko da Xi Jinping ya kai zuwa ƙetare, tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasar Sin, kuma wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da ra’ayin “Sabon Nau’in Alaƙar Ƙasa Da Ƙasa”. Tun daga wannan lokacin, an sha bayyana “Sabon Nau’in Alaƙar Ƙasa Da Ƙasa ” a tarukan ƙasa da ƙasa, hakan ya zama matsayin da ƙasar Sin ke dauka da babbar ƙa’idar da take bi wajen raya dangantakar ƙasa da ƙasa.

A ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2021, lokacin da Xi Jinping ya halarci babbar muhawarar babban taron MDD karo na 76 ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, ya sake jaddada cewa, dole ne mu ƙarfafa hadin kai, da aiwatar da ra’ayin dangantakar ƙasa da ƙasa ta mutunta juna da samun nasara tare.

“Nasarar da wata ƙasa ta samu, ba ya nufin dole wata ƙasa ta gaza ba, duniya tana iya ba da cikakkiyar damar samun ci gaban dukkan ƙasashen. Dole ne mu tsaya kan tattaunawa maimakon adawa da juna, da juriya maimakon wariya, da gina sabon nau’in hulɗar ƙasa da ƙasa da ke mutunta juna, da adalci, da haɗin gwiwar cin nasara tare, da faɗaɗa fannonin samun moriyar juna.”

Fssarawa: Bilkisu Xin