ECOWAS ta tusa Gwamnatin Sojin Mali gaba

Daga AISHA ASAS

Tun bayan yin murabus da shugaban riƙon ƙwaryar Mali, Bah Ndaw da firaministansa Moctar Ouane kwanaki biyu bayan da soji suka yi mu su juyin mulki, kana suka tsaresu, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya da ma ECOWAS da sauran ƙasashen duniya, suka buƙaci a sake su kana a mayar da ƙasar kan turbar mulkin dimukuraɗiyya.

Maimakon a lokacin mutane su nuna farin ciki da jin daɗin kifar da gwamnatin kamar yadda su ka yi murna da hamɓarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara; a wannan karo sai su ka fita zanga-zangar nuna ƙyama ga matakin ƙwace mulkin da sojojin suka sake yi. 

Rahotanni sun nuna tun daga wancan lokacin Mali ta shiga wani yanayi na rashin tabbas da kuma fara cire rai da mulkin dimukuraɗiyya a ƙasar cikin ƙanƙanin lokaci, duk da ƙungiyar ECOWAS da wasu ƙungiyoyin ƙasashen duniya sun yi ta faɗi tashin ganin lamarin ya daidaita amma abin ya ci tura.

Ko a Lahadin da ta gabata ma, Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) tare da ƙungiyar ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin CFA wato UEMOA sun ɗauri aniyar sanya wa Ƙasar Mali sabbin takunkumi tare kuma da janye dukkan jakadunsu da kuma rufe iyakokin ƙasa na sama da ƙasa.

Wannan hukunci dai wani ɓangare ne na sakamakon babban taron shugabannin ƙasashe da gwamnatin ECOWAS da aka gabatar a Accra, babban birnin Ƙasar Ghana.

Wasu daga cikin matakan da taron ya ɗauka sun haɗa da; rufe iyakokin Mali da illaririn ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita. Sannan sun amince da hana ikon taɓa kuɗaɗen da ƙasar ta mallaka ga sojojin da ke mulki, ta hanyar daskare asusun ajiyar ƙasar da ke a babban bankin ƙasashe masu amfani da kuɗin CFA wato BECEAO.

Sai dai taron ya tabbatar za a ci gaba da fitar da kuɗaɗen siyan magunguna da kuma buƙatun gaggawa. Har ila yau, taron ya ce, daga yanzu an haramta hada-hadar kuɗaɗe tsakanin Mali da sauran ƙasashen yankin da suke ƙarƙashin inuwar guda 14.

Duk da cewa, wasu na ganin hukuncin ya yi tsauri, a cewarsu, me ya yi zafi shi ba wuta ba. Sai dai waɗanda suka san tushe da asali na wannan taƙaddama, sun amince komai ya samu ɗan yaƙi kwaɗayinsa ne ya jawo masa, domin Ƙasar Mali ta daɗe tana baɗa kura ga jama’arta, yayin da ƙungiyoyin ke mata hannunka mai sanda, da kuma ja mata kunne, lura da ta yi nisa, ba ta jin kiran da suke mata ne ya sanya suka yanke wannan hukunci da suke fatan ya kawo ƙarshen mulkin soja, tare kuma da sakar wa dimokuraɗiyya mara ta yi fitsari.

Wasu na ganin janye jakadun da aka yi na da nasaba da korar jakadan ita ECOWAS da gwamnatin ta yi a watannin baya, a kan zargin yi mata katsalandan cikin harkokin gida. A ganinsu wannan hukuncin da suka yanke ne ya bar baya da ƙura. Idan kuwa anyi duba da hujjoji da dalilan da ƙungiyar ke da kan mulkin zai sa mutane da dama su yi na’am tare da jin daɗin wannan takunkumin da ta laƙaba ma su.

Duk da ganin matakan a matsayin hanyar da za ta kawo ƙarshen matsalar, ga dukkan alama ba haka yake a mahangar gwamnatan sojin ƙasar ta Mali ba, domin rahotanni sun tabbatar da sun yi biris da takunkumin da aka maƙala ma su, ko ta hanyar jan ƙafa da suke yi wurin miƙa mulki ga farar hula, a cewarsu, a ba su shekara biyar kafin su miƙa mulkin ga fararen hula.

Ko a baya-bayan nan, gwamnatin sojin ta ce, a shirye ta ke ta yi sulhu da ECOWAS, shugabban mulkin sojin Mali, Assimi Goita, ya bayyana hakan. Wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da rasa uwar goyonsu da suka yi, wato Faransa, wadda ta bayyana goyon bayanta ga hukuncin na ECOWAS. Faransa ta bayyana amincewarta ga takunkumin da aka sa wa ƙasar a wani taro da ya gudana a zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. 

Ƙungiyar ta ECOWAS ta goyi-bayan katse asusun tallafin da ake bai wa ƙasar da kuma daskare asusun ajiyarta. Wanda suke fatan ya zama silar dawowar dimokuraɗiyya a ƙasar.

Duk da cewa, shugabbanin na mulkin soji sun cancanci wannan tsatsauran matakai da aka ɗora, wasu na ganin hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba, domin dai ga dukkan alama ba su da niyar sauka daga ragamar mulkin, wanda ake hasashen jama’ar ƙasar ne za su jigata. Sulhun da suka bayyana sun shirya yinsa ba ya da nasaba da karaya ko jin tsoron tsatsauran matakan da aka ɗauka kansu, domin sun bayyana hakan ne jim kaɗan bayan sanar da cewa, akwai yiwar a ɗauki tsayin shekaru biyar kafin su miƙa mulki ga farar hula.

Da wannan ne za mu iya cewa, gwamnatin sojin Mali na bisa dokin na ƙi da ta hau tun a farkon fara rigimar, kuma akwai yiwar tsauraran matakan da ECOWAS ta ɗauka ba za su tanƙwarar da su ba, sai an kai ruwa rana.