ECOWAS za ta karrama Buhari kan bunƙasa dimokuraɗiyya

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta ce ta kammala shirinta don karrama Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da lambar yabo saboda nasarorin da ya samu a fannin tsaro da dimokuraɗiyya.

Wannan na zuwa ne yayin da Buhari yake shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, shi ne ya bayyana haka a wajen taron ƙawancen da suka yi yayin da suka haɗu a wajen Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a Doha, babban birnin Qatar.

Shugaba Embalo ya ce Buhari ya taka rawar gani fiye da yadda ake zato wajen mara wa gwamnatin dimokuraɗiyya baya a shiyyar Afirka ta Yamma.

Don haka Shugaban na ECOWAS ya ce za a karrama Buhari tare da ɗaukaka sunansa a sabon hedikwatar ƙungiyar da ake ginawa a Abuja bayan kammalawa domin ‘yan baya su san irin gudunamwar da ya bayar ga cigaban yankin da kuma zama abin koyi a gare su.

A nasa ɓangaren, Shugaba Buhari ya yi maraba da hakan, tare da jaddada cewar dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi dacewa wajen shugabanci da kuma haɗa kan al’umma.