Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

An rantsar da Eiditan Jaridar Blueprint na intanet, Amb. Ikenna Okonkwo, a matsayin Sakataren Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Nijeriya.

Amb. Okonkwo ya gaji wannan matsayi ne a wajen Mr. Jude Opara bayan da ya tsaya takarar neman muƙamin ba tare da hamayya ba.

Haka nan, Mr. Isaiah Benjamin na Jaridar Leadership shi ne wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙungiyar SWAN na ƙasa bayan babban taron da ƙungiyar ta gudanar a ranar Alhamis, 13 ga Yulin 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *