EFCC ba ta tasa ƙeyar Kakakin NAHCON, Fatima Usara ba – Bincike

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wani bincike da Blueprint Manhaja ta gudanar ya nuna cewa, babu ƙamshin gaskiya a rahoton da aka wallafa da ke nuna cewa, jami’an Hukumar EFCC sun yi dirar mikiya a Hukumar Kula Da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) suka yi awon gaban da Kakakin Hukumar, Hajiya Fatima Usara, ba gaskiya ba ne.

Binciken ya nuna cewa, tun asali EFCC ta nemi wasu bayanai ne na wasu shekaru da suka gabata game da hukumar a ƙarƙashin ofishin tsohon kakakin NAHCON, wanda kuma odishin kakakin ta yanzu ta miƙa wa EFCC ɗin, kamar yadda ta buƙata.

Idan za a iya tunawa, wasu jaridu sun bayar da rahoton cewa, a Talatar da ta gabata aka tasa ƙeyar kakakin da misalin ƙarfe 11:00 na safe. To, amma binciken Blueprint Manhaja ya tabbatar da cewa, a tsakanin Azahar da La’asar Fatima Usara tare da wasu jami’an NAHCON suka ziyarci ofishin EFCC suka miƙa bayanan da ake buƙata, sannan suka baro hukumar nan take.

“Babu wanda ya kama jami’an NAHCON ko ya tsare su, kuma ba sabon abu ba ne EFCC ta nemi bayanai daga kowacce hukuma ta gwamnati ko kamfani mai zaman kansa a lokacin da ta ke gudanar da bincikenta,” inji majiyarmu.

Idan za a iya tunawa, EFCC ta taɓa tsare tsohon Shugaban NAHCON, Alhaji Jalal Arabi, wanda ya bar shugabancin hukumar bayan kammala aikin hajjin da ya gabata na 2024, bisa zargin wadaƙa da biliyoyin Naira.

Da aka tuntuɓi Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya yi alƙawarin bayar da cikakken bayani idan suka kammala bincike.

Ita ma Hukumar NAHCON, ta hannun mai magana da yawunta, Fatima Usara, ta nuna ba ta son yin magana da manema labarai kan aikin da ba hukumarta ce ke gudanar da bincike akai ba.