EFCC na farautar ɗan takarar sanatan Kano a APC, A.A Zaura kan badaƙalar miliyan N576.6

Daga WAKILINMU

Hukumar EFCC ta ce za ta cafke ɗan takarar sanata na Kano ta tsakiya na Jam’iyyar APC, AbdulKareem AbdulSalam Zaura.

EFCC na neman Zaura ta kama ne bisa zargin almundahanar Dalar Amurka miliyan 1.3, kwatankwacin miliyan N576.6.

Lauyan EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana haka ranar Litinin yayin da aka dawo ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun da ke zamanta a Kano.

Sai dai zaman shari’ar na wannan rana bai yiwu ba sakamakon Alƙalin kotun ya halarci wanibtaron ƙasa a wajen Kano.

Lauyan hukumar ya ce, kamata ya yi ɗan takarar ya kai kansa ga hukumar ta EFCC.

A cewar lauyan, “Muna neman Zaura ruwa a jallo kuma za mu tsare shi da zarar muka same shi.

“Da ma kamata ya yi yana tsare a hannunmu, kotu ma ta tabbatar da hakan, amma ina mai tabbatar muku za mu kama shi mu kawo shi kotu kafin zama na gaba a ranar 30 ga Janairu, 2023,” in ji lauyan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *