EFCC ta bankaɗo makarantar koyon yahoo a Edo

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC), ta ce ta kama mutane 25 waɗanda take zargin masu damfara ne ta yanar gizo a wani wuri da ake kyautata zaton na horar da damfara ne a Benin, babban birnin Jihar Edo.

A cikin wani rubutu da ta ɗora a shafinta na X, hukumar ta ce ta yi nasarar yin hakan ne a ranar Alhamis ta hanyar amfani da jami’anta na Benin.

Ta ce kamen ya biyo bayan samun wasu sahihan bayanan sirri ne da ke nuna cewa ana amfani da wani gini a matsayin wurin koyar da damfarar yahoo ko kuma horar da masu son ƙwarewa a sauran hanyoyin damfara ta intanet.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, EFCC ta ce ta kuma gano wasu kaya a lokacin samamen nata, waɗanda suka haɗa da dalla-dallan motoci guda shida, da kwamfutoci da kuma wayoyi.

“Nijeriya dai ta yi ƙaurin suna a harkar damfara ta intanet a duniya”, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.