EFCC ta kama Akanta-Janar da wasu kwanaki kaɗan kafin Obaseki ya mika mulki a Edo

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake ƙasa da makonni biyu da zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebhol zai karɓi mulki daga hannun Gwamna Godwin Obaseki, Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC ta cika hannu da Akanta-Janar na jihar, Julius O. Anelu da wasu jami’ai huɗu na ofishin asusun jihar.

An kama su ne a ranar Alhamis inda a aka tsare su a ofishin hukumar dake Benin, babban birnin jihar.

EFCC ta kama su ne don dakatar da zuƙar wasu kuɗaɗe na Kasafi da ake zargin Majalisar Dokokin jihar ta tabbatar da su makonni biyu kafin miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati.

Wata majiya ta ce hakan ya haifar da tsaiko ga harkokin gudanar da gwamnati inda ta kasa biyan ma’aikata wasu kuɗaɗe da na ƴan fansho da ƙuɗaɗen tsaro da sauran su.

Hukumar za ta tsare mutanen ne har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba, wanda a lokacin ne za sabuwar gwamnati za ta fara aiki.