EFCC ta kama tsohon abokin takarar Atiku, Okowa kan zargin badaƙala

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an hukumar EFCC sun cika hannu da tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa kan zargin sauya akalar Naira Tiriliyon 1.3 daga asusun Gwamnatin Tarayya waɗanda ke wakiltar kaso 13 na kuɗin asusun daga 2015 zuwa 2023.

A ranar Litinin ne aka kama tsohon gwamnan, a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas a lokacin da ya amsa gayyatar hukumar a offishinta dake birnin kan al’amarin.

Ana zargin Okowa ne da ƙin bada asusun da aka ware don sanya kuɗaɗen, sannan da kuma wasu biliyan 40 na hannun jarin da ya mallaka a ɓangaren gas na ‘UTM Floating Liquefied Natural Gas’.

An zargi cewa, an yi amfani da su ne ta wasu hanyoyi inda ake binciken waɗansu rukunin gidaje a Abuja da Asaba da ake zargin sa da sayan su.

Okowa shi ne abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.