EFCC ta tura jam’ianta jihohi don sanya ido kan zaɓen gwamnoni

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, ta tura jami’anta zuwa jihohin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi domin sanya ido kan zaɓen ranar Asabar.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce, jami’an hukumar sun isa wuraren da aka tura su don sauke nauyin da aka ɗora musu.

Majiyarmu ta ce jami’an da aka tura Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin ACEII Mustapha Abubakar, sun isa jihar inda suka gana da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, J.A Ogundele.

Haka nan, sun ziyarci Kwamishinan Zaɓe na jihar, Ahmed Yusha’u Garki.

Haka ma lamarin yake ga jami’an da aka tura Jihar Nasarawa ƙarƙashin jagorancin ACE II Adeniyi Adebayo, su ma sun samu ganawa da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar a Lafiya, babban birnin jihar.

Shugaban EFCC na Ƙasa, Abdulrasheed Bawa, ya yi kira ga jami’an hukumar da su nuna ƙwarewa wajen a ikinsu yayin zaɓen na gwamnoni da na majalisun jihohi da ke gudana a wannan Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *