EFCC ta yi awon gaba da shugaban KASUPDA yana tsakiyar ganawa da ma’aikata

Daga MAHDI M. MUHAMAD a Abuja

A ranar Litinin da ta gabata ne Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC), sun cafke shugaban hukumar raya birane na jihar Kaduna (KASUPDA), Malam Ismail Umar Dikko.

Shugaban wanda ya yi fice wajen rusa kadarorin jama’a kuma kowa ke shakkansa, an cafke shi ne yayin da yake ganawa da ma’aikatansa.

Kafin ya zama shugaban hukumar a 2019, Ismail ya kasance mataimaki na musamman ga gwamna Nasir El-Rufai.
Shigowar jami’an EFCC cikin harabar tare da baqar mota ƙirar Hilux Toyota da farko ya haifar da fargaba a tsakanin ma’aikatan, musamman saboda suna da maƙamai sosai.

Majiyar ta ce, tun da farko ma’aikatan KASUPDA sun yi ƙoƙarin hana EFCC fita da shugaban ta su, inda tsaro a ƙofar gidan ya hana motar fita.

Shugaban ya ba da umarnin a ƙyale su su fita kuma nan take aka kai shi ofishin shiyyar Kaduna na EFCC.

Wata majiya da ke kusa da lamarin ta yi nuni da cewa, Shugaban ya yi watsi da gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta yi masa a baya, don haka suka shiga harabar hukumar ba tare da sun sani ba a ranar Litinin.