EFCC za ta fara sa ido kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da ake ƙoƙarin dakatar da duk wata harƙallar ƙananan hukumomi daga hannun gwamnonin jihohi, Nijeriya za ta fara biyan kuɗaɗen rabon ƙananan hukumomi kai tsaye a watan Nuwamba 2024.

Hakeem Ambali, shugaban ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta ƙasa (NULGE), ya tabbatar da hakan wata hira da manema labarai a ranar Lahadi.

Hukumar Da Ke Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Tu’annati EFCC, ta yi alƙawarin sanya ido sosai kan harkokin kuɗi na dukkan shugabannin ananan hukumomi 774, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen da ake fitar da su daga kason kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke yi cikin gaskiya da adalci. 

Ana kallon wannan mataki a matsayin wani muhimmin mataki na aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, kamar yadda Kotun ƙoli ta amince da shi a baya-bayan nan.

Batun cin gashin kansa ya taso ne a cikin watan Mayu lokacin da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ta shigar da ƙara domin hana gwamnoni yin katsalandan kan kuɗaɗen da aka tanada ga ƙananan hukumomin.

Kotun ta ce, bai kamata gwamnoni su rusa kansiloli da aka zaɓa ba ko kuma su kafa kwamitocin riƙon kwarya, saboda yadda tsarin mulki ya tanada na zaɓen ƙananan hukumomi.

A cikin wani muhimmin hukunci na Yuli 2024, Kotun Koli ta yanke hukuncin ba da yancin kai na kuɗi ga ƙananan hukumomi, tare da hana gwamnoni sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomin.

Mai shari’a Garba Lawal, wanda ya jagoranci kwamitin Kotun ƙoli, ya bayyana rashin tura waɗannan kuɗaɗe kai tsaye ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, sannan ya umurci Akanta-Janar da ya saka kason kuɗaɗen kai tsaye a asusun ƙananan hukumomi.

Bayan da aka yanke hukuncin ne gwamnatin tarayya ta ɗage zamanta na tsawon watanni uku domin shawo kan matsalolin albashi da ayyuka.

Don tallafa wa sauyin mulki, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin ma’aikatu mai mambobi 10 don aiwatar da hukuncin Kotun Koli.

Kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya jagoranta, ya gabatar da sakamakonsa a ranar 13 ga watan Oktoba. 

Mambobin kwamitin sun haɗa da manyan jami’ai irin su Wale Edun, ministan kudi, da Olayemi Cardoso, gwamnan babban bankin Nijeriya, da kuma wakilai daga hukumomin jiha da na ƙananan hukumomi.

Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa sama da ƙananan hukumomi 160 a jihohi takwas ne har yanzu ba su gudanar da zaɓukan da ake buƙata ba, inda gwamnatin tarayya ta yi gargaɗin cewa za a iya kwace musu kason su idan har aka ci gaba da jinkirin zaɓe.

Sai dai Ambali ya tabbatar da cewa an shirya fara biyan kudaden rabon kai tsaye a watan Nuwamba, inda ƙungiyar NULGE da sauran ƙungiyoyin suka buƙaci fadar shugaban aasa da ta hana kuɗazen jihohin da suka ƙo aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Ambali ya ƙara da cewa, “Muna so mu tabbatar da cewa komai ya yi daidai domin gujewa matsala, musamman ganin yadda wasu gwamnoni ke ƙoƙarin riƙe madafun ikon ƙananan hukumoki, kamar yadda ake gani a jihar Abia.”

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya jaddada shirin hukumar na sa ido kan yadda ake gudanar da kasafin kuɗi a faɗin ƙananan hukumomin, da nufin tabbatar da bin diddigi.

Ya soki tasirin da gwamnatocin jihohi ke da shi kan albarkatun ƙananan hukumomi, inda ya ba da misali da tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku kan zargin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

A cewar Olukoyede, EFCC ta ƙara faɗaɗa ayyukan ta a faɗin ƙasar, da nufin aiwatar da tsauraran matakai a cikin majalisar ƙananan hukumomi tare da daƙile da duk wani abu da ya shafi almubazzaranci.

A halin da ake ciki dai, wasu gwamnonin sun buƙaci ƙarin lokaci don fara biyan kason kai tsaye, wanda zai ƙare a watan Oktoba.

Daudu Clifford, shugaban ƙungiyar NULGE na jihar Edo, ya bayyana cewa duk wani jinkirin da ya wuce watan Nuwamba, zai saɓa wa hukuncin ƙotun Koli, wanda ke da alhakin sakawa shugabannin ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kaingsaye ba ta hannun gwamnatocin jihohi ba.

ƙungiyar ƙananan Hukumomin Nijeriya, ALGON, da sauran wakilan yankin sun tabbatar da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen.

Aminu Kaita, Shugaban ALGON na ƙasa, ya bayyana cewa wa’adin da aka sanya na watan Oktoba zai tabbata, kuma majalisu suna aiki tuƙuru don biyan buƙatu.

Sai dai wasu daga cikin ƙananan hukumomin da suka haɗa da na Zamfara da Sokoto suna jiran tantancewa kan tsarin rabon kuɗaɗen, yayin da wasu suka ƙi cewa uffan har sai an bayyana tasirin manufofin.

Yayin da ranar da za a fara watan Nuwamba ke gabatowa, ana sa ran ƙananan hukumomin za su fuskanci ingantacciyar ‘yancin cin gashin kai, wanda ke nuna wani sauyi ga mulkin kai wanda zai iya kawo gagarumin ci gaba ga al’ummar Nijeriya.