Ekiti 2022: Masu zaɓe sun yi tururuwa zuwa rumfunan zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Ekiti sun ce, jama’a sun yi tururuwa a safiyar Asabar don zuwa kaɗa ƙuri’a a rumfunna zaɓe a faɗin jihar.

Haka nan, bayanan sun ce an ga jami’an zaɓe sun isa rumfunan zaɓen da aka tura su tun da misalin ƙarfe 7 na safe.

A wannan Asabar ɗin ce al’ummar Jihar Ekiti ke kaɗa ƙuri’a domin zaɓen gwamnan da zai ci gaba da jan ragamar mulkin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa bayan kammala wa’adin Gwamna Kayode Fayemi.

Ya zuwa haɗa wannan labarin, tun an kammala kaɗa ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓen, har ma an soma fitar da sakamakon zaɓen.

An ga Gwamnan Jihar, Kayode Fayemi, a lokacin da shi ma ya tafi ya kaɗa ƙuri’arsa a matsayinsa na dan jihar.

Yayin kaɗa ƙuri’ar tasa, Fayemi ya yi kira ga talakawansa da su bai wa jami’an zaɓe da na tsaro haɗin kan da ya dace, kana su yi mafani da wannan dama wajen zaɓen ɗan takarar da ya dace ya zama gwamnan jihar.

Masu zaɓe a cikin layi

‘Yan takara 16 ne ke fafatawa a zaɓen tare da mace ɗaya a tsakaninsu, Mrs Kemi Elebute-Halle daga Jam’iyyar ADP.

Sauran jam’iyyun da zaɓen ya shafa sun haɗa da; ACCORD, AAC, SDP, YPP, ZLP, ADC, APC, APGA, APM, APO, LO, NNPP, NRM, PDP da kuma PRP.

Masu zaɓe a jihar kimanin su 749,065 da hukumar zaɓe ta yi wa rijista ne ake sa ran su zaɓi wanda zai ci gaba da riƙe musu jihar a tsakanin shekaru huɗu masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *