Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai Bai Wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Shawara Kan Harkokin Shari’a, Ahmed El-Marzuk, ya yi murabus daga kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙasa.
Majiyar Blueprint Manhaja ta ta samu labarin cewa ya yi murabus ne a ranar Larabar da ta gabata, sakamakon dagewar da wasu abokan aikinsa suka yi na cewa ba zai iya ci gaba da zama a ofis ɗin ba saboda wasu zarge-zargen da ake masa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bisa abubuwan da ke faruwa a cikin babbar jam’iyyarmu ta APC, inda mai girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ajibola Basiru ya zama shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakataren ƙasa da kuma sake fasalin jam’iyyar.
Ofisoshi na haɗin kan ƙasa da isassun wakilcin yanki, mashawarcin kan harkokin shari’a na qasa ya ga ya dace ya ajiye muƙaminsa a cikin jam’iyyar domin ba da damar sake fasalin shugabancin jam’iyyar.”
El-Marzuq ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran jami’an jam’iyyar saboda “damar” ta yin hidima.