El-Rufai ga Hukumar JAMB: Ku daina bai wa ɗaliban Arewa maki na musamman

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya yi kira ga Hukumar Shirya Jarabawar Sahare Fagen Shiga Manyan Makarantu (JAMB) a kan ta daina bai wa ɗaliban Arewacin Nijeriya da suka rubuta jarabawarta maki na musamman.

El-Rufai ya yi wannan kira ne a lokacin da ake hira da shi a wani shirin tashar ChannelsTV a safiyar Litinin da ta gabata.

Ya ce ba yana nufin a bai wa ɗaliban ƙasa da makin da aka ƙayyade ba ne, amma dai a ba su makin daidai da yadda ake bai wa takwarorinsu a sauran sassan ƙasa domin su iya gogayya a duk inda suka tsinci kansu.

Gwamnan ya ce matakin rufe makarantun jihohin da ya ɗauka, ya yi hakan ne saboda harkokin ‘yan fashin da suka addabi jihar.

Haka nan, ya ce Arewa ce koma-baya a sha’nin ilimi tun lokacin samun ‘yancin kan ƙasa zuwa yau duk da irin alfarmar makin da yankin ke samu a wajen JAMB. Ya ci gaba da cewa, hasali ma wannan ya sanya jma’ar yankin zama ragwage.

Don haka ya ce a tunaninsa kamata ya yi a ƙarfafa wa jama’a su zama masu ƙwazo ta yadda za su iya gogayya da takwarorinsu a ko’ina, “Kuma a shirye muke mu kimtsa ‘ya’yanmu a Kaduna su zama masu ƙwazo don su iya gogayya da takwarorinsu a ko’ina.”

Yana mai cewa sun rufe wasu makarantun jihar ne bisa shawarwarin tsaro, kuma za a yi hakan ne na wasu watanni don bai wa jami’an tsaron zarafin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Tare da cewa, suna da yaƙinin nan da makonni biyu za su soma buɗe makarantun a hankali.

El-Rufai ya ce matsalar tsaro ta haifar wa fannin ilimin jihar cikas, lamarin da ya yi sanadiyar rufe makarantu sama da 5,000 a faɗin Kaduna.