El-rufa’i ya rasa kujerun sanatoci uku a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i ya rasa kujerun sanatoci na dukkan shiyyoyi uku da ke faɗin jihar.

El-rufa’i wanda na gaba-gaba ne a Jam’iyyar APC kuma mai faɗa a ji a cikinta, ya rasa kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya wanda Muhammad Sani Dattijo na APC ke takara da abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP, wato Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr LA.

Dattijo dai ana ganin ɗan lele ne a gwamnatin Jihar Kaduna, domin ya riƙe manyan muƙamai a gwamnatin El-rufa’i, ciki har da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin jihar, da kuma Kwamishinan Kuɗi, amma Lawal Adamu na Jam’iyyar PDP ya liƙa shi da ƙasa a zaɓen na ranar Asabar.

Mr LA dai ya kada Dattijo ne da zunzurutun ƙuri’u har 225,066. Inda shi kuma Dattijo ya samu ƙuri’u 182,035.

Umar Ahmad Tijjani na Jam’iyyar NNPP ya samu quri’u 24,395, yayin da Ibrahim Muhammad Sani na Jam’iyyar Labour ya samu ƙuri’u 8,7510.

A Shiyya ta 1 kuwa, Barista Khalid Ibrahim Soba na Jam’iyyar PDP ne ya liƙa ɗan takarar APC mai ci, Abdu Kwari da ƙasa, a yayin da Sunday Marshal Katung na PDP ya lashe zaɓen Sanatan Kudancin Kaduna.

Sai dai kuma ɗan Gwamnan na Kaduna, wato Bello El-rufai da yake takarar kujerar majalisar tarayya a Kaduna ta Arewa ya lashe kujerar, inda ya kada Sama’ila Suleiman mai ci na Jam’iyyar PDP.