El-Rufai ya roƙi ’yan PDP, Labour Party da sauran jam’iyyu su haɗe da SDP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya buƙaci ‘yan jam’iyyar adawa da suka haɗa da PDP, Labour Party da sauransu da su shiga jam’iyyar SDP a yunƙurinsu na ganin sun kawar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, yayin da ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC.

“Ba tare da nuna kyama ga wannan shawarar ba, a matsayina na ɗan jam’iyyar SDP, zan mayar da hankali wajen yin cuɗanya tare da jawo hankalin sauran shugabannin jam’iyyun adawa da su haɗa kai da mu, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya guda ɗaya domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a duk zaɓukan da za a yi tsakanin yanzu zuwa 2027, da yardar Allah.

“Saboda haka, ina kira ga dukkan magoya bayanmu da ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su haɗa kai da mu a jam’iyyar SDP yayin da muke ƙoƙarin ganin Nijeriya ta zama abin alfahari ga ‘yan Afirka da kuma baƙar fata.”

A cikin jawabinsa, El-Rufai ya amince da gudunmawar da ya daɗe yana baiwa jam’iyyar APC amma ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda jam’iyyar ke tafiya a halin yanzu.

Ya ce, “Na yi wa jam’iyyar APC hidima kuma na ba da gudunmawa wajen bunƙasar ta, amma jam’iyyar ta karkata akalarta, wanda hakan ya sa na tsaya a kan tunanin waɗanda suka kafa ta.