Elon Musk ya sake ƙwato kambunsa na mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Daga AMINA YUSUF ALI

Elon Musk ya sake dawowa matsayinsa na mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya bayan ya tara maƙudan kuɗaɗe har Dalar Amurka biliyan $6.98 a cinikin awoyi takwas kacal.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne dai attajiri Musk ya rasa muƙamin nasa na mai arzikin duniya bayan da wani Bafaranshen attajiri mai suna Bernard Arnault ya yi masa ƙafar baya tare da ture shi, kuma ya haye ƙaragarsa ta mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya, a ranar 8 ga watan Disambar, 2022.

Al’amarin da ya jawo Musk ya rasa wancan matsayi nasa ba ya rasa alaƙa da al’amuran dake kewaye da cinikin kamfanin dandalin yanar gizo na Tiwita. Abinda ya tilasta wa attajirin sayar da wasu hannayen jarinsa na kamfanin motocinsa na Tesla, lamarin da ya yi sanadiyyar kawo raguwa a dukiyarsa.

Musk ya sha ƙoƙarin ganin ya koma kan matsayinsa, amma abin ya ci tura domin dukiyar abokin karawar tasa, Arnault ta yi ta ƙara bunƙasa.

Sai kuma kwatsam! A ranar Litinin 27 ga watan Fabrairu Allah ya yi ikonsa. Domin hannun jarin kamfanin Tesla ya bunƙasa matuƙa zuwa kaso 100 bisa 100 bayan cinikin awoyi 8 kacal.

Wannan bunƙasar hannun jari ta taimaka wa Musk matuƙa wajen samun Dalar Amurka har biliyan $6.98, abinda ya sanya jimillar qarfin arzikin biloniya Musk ya ƙaru zuwa Dalar Amurka biliyan $187 kamar yadda rahoton Bloomberg ya rawaito.

Kodayake shi ma Bernard Arnault, mamallaki kuma shugaban zartarwa na kamfanonin LVMH Moët Hennessy Louis Vuitton, mafi girman kamfanin duniya na sayar da kayan ado da alatu shi ma dai a ranar litinin ya samu Dalar Amurka biliyan $3.69 amma hakan bai hana shi shan kaye ba a hannun Elon Musk.

A yanzu haka ƙarfin arzikin Bernard Arnault ya kasance biliyan $185 wato Musk ya kere shi da Dalar Amurka har biliyan 2.