Emefiele ya faɗa a komar DSS sa’a guda bayan dakatar da shi

Daga BASHIR ISAH

Hukumar tsaro ta DSS ta tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, bisa zargin ta’addanci.

Wannan na zuwa ne ƙasa da sa’a guda bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, dakatarwar da Shugaba Tinubu ya yi wa Emefiele daga ofishinsa ta fara aiki ne nan take.

Kamar dai yadda sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ta nuna a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *