
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne Kotun Alƙalanci ta Wasanni ta umarci Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), da ta ƙyale Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Kamaru, Samuel Eto’o ya zama ɗan takara a majalisarta ta zartaswa.
CAF ta ƙi amincewa da tsayawa takara da tsohon gwarzon ɗan wasa na Afirka ke ƙoƙarin yi, kasancewar shi ne shugaban hukumar ƙwallon ƙasarsa tun a shekarar 2021.
A mako na gaba ne CAF za ta gudanar da zaɓe a babban zaman da ta shirya.
Eto’o mai shekaru 43, wanda kuma tsohon ɗan wasan ƙungiyar Barcelona ne, na hali na rikici da ma’aikatar wasanni ta Kamaru, lamarin da ya sa ya ɗaukaka ƙara a babbar kotun wasannin.
A ranar 12 ga watan Maris ne za a gudanar da zaɓen, inda wata majiya daga ƙasarsa ta ce Eto’o na harin muƙamin mataimakin shugaban CAF ne.