Etsu Nupe ya yi jajantawa kan rasuwar Sarkin Kagara

Daga UMAR M. GOMBE

Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya bayyana rasuwar marigayi Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin da masarautar Kagara da jihar Neja da ma ƙasa baki ɗaya.

Etsu Nupe ya faɗi haka ne ga manema labarai a garin Minna a Larabar da ta gabata a lokacin da yake jajantawa game da rasuwar basaraken. Tare da cewa rasuwar marigayin ta haifar da wagegen giɓin da iya cike shi sai an yi da gaske.

Da wannan ne sarkin ya ce, “A madadin Majalisar Sarakunan Gargajiya, ina jajantawa ga Gwamna Abubakar Sani Bello, Masarautar Kagara da al’ummarta da ma jama’ar jihar Neja baki ɗaya dangane da rasuwar sarkin Kagara wanda ya gaji kakanninsa. Wanda ya zama sarki mai daraja ta biyu 1982 kana daga bisani ya zama sarki mai daraja ta ɗaya a 199.”

A cewarsa, marigayin ya ƙaunaci al’ummar masarautarsa ba tare da nuna wani bambanci ba. Tare da bayyana shi a matsayin mutum mai tsoron Allah wanda lamarin talakawansa na gaba da komai a gare shi.

Kazalika, Etsu Nupe ya ce marigayin ya yi rayuwa abar koyi ga jama’a, musamman ɗabi’ar yafiya da yake da ita.

Basaraken ya yi kira ga iyalan marigayin da su yi riƙo da kayawawan mu’amalolin da ya bari, musamman al’amarin haɗin kai ba tare da nuna bambancin yare, ko na addini, ko kuma na siyasa ba.