Everton ta ɗauki Ashley Young

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Everton ta ƙulla yarjejeniya da Ashley Young kan kwantiragin shekara ɗaya bayan ya bar Aston Villa a bazara.

Ɗan wasan, mai shekaru 38, ya zama ɗan wasa na farko da Everton ta saya a ƙarƙashin kocinta Sean Dyche kuma har ya riga ya haɗe da sauran ‘yan wasan ƙungiyar a sansanin da suke shirin tunkarar kakar wasa ta bana a ƙasar Switzerland.

An fahimci cewa Young ya fara tattaunawa da Luton kuma waɗansu ƙungiyoyi a Saudiyya sun nuna sha’awarsu, amma daga baya ya yanke shawarar komawa Everton.

Mai tsaron bayan ya lashe gasar Europa da League Cup tare da Manchester United kuma ya buga wa Ingila wasanni 39, inda ya buga wasa a gasar kofin duniya ta 2018 da Croatia ta doke su a wasan kusa da na ƙarshe.

Young ya buga wasanni sama da 700 a kulob da kuma ƙasa, ciki har da wasanni 32 da ya buga wa Villa a kakar wasan da ta wuce, kuma zai kai ƙwarewarsa qungiyar Everton da ta tsallake rijiya da baya a kakar wasanni biyu da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *