Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fitaccen dɗan siyasa kuma mai sukar jam’iyyar APC, Buba Galadima, ya zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da haddasa faɗuwar farashin kayan masarufi da gangan don durƙusar da tattalin arzikin Arewacin NIjeriya.
Galadima ya yi wannan ikirarin ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon DCL Hausa a kwanakin baya, inda ya yi zargin cewa manufar wani ɓangare ne na dabarun raunata tattalin arzikin Arewa.
Rikicin tsadar rayuwa a Nijeriya kwanan nan ya samu sauƙi a karon farko tun bayan da shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayun 2023.
Wani bincike na kasuwar Nijeriya ya nuna cewa sama da kashi 40 cikin 100 an samu raguwar farashin abinci tsakanin Disamba 2024 da Maris 2025.
Binciken da Business Day ta gudanar ya ce a yanzu haka ana sayar da matsakaitan farashin buhun shinkafa na waje mai nauyin kilogiram 50 a kan Naira 85,000, ya danganta da iri da girman hatsin da aka sayar da ita watanni biyar da suka gabata, a Legas, babban birnin tattalin arzikin Nijeriya.
A yanzu dai ana sayar da shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan Naira 95,000 a birnin, inda aka sayar da ita Naira 105,000 watanni uku da suka wuce.
Farashin babban kwandon tumatir ya ragu da kashi 70 cikin 100 a Legas daga matsakaicin Naira 120,000 zuwa N35,000. A shekarar 2024, ‘yan Nijeriya ba za su iya sayen tumatur ba sakamakon tashin farashi inda suka koma amfani da busasshen barkono, sun samu sauƙi.
Hakazalika, kwando mai lita 4 na garri a yanzu ana sayar da shi akan Naira 2,500 daga matsakaicin Naira 3,500 watanni biyar da suka gabata, wanda ke nuna an samu ƙarin kashi 28.5 cikin ɗari. Buhun Garri mai nauyin kilogiram 60 a yanzu ana sayar da shi akan N37,500.
A Fatakwal da Abuja farashin albasa ya ragu. Yanzu haka ana iya sayen Albasa guda shida zuwa 10 da N1000 saɓanin guda uku ko huɗu a farashi ɗaya watanni uku da suka wuce.
Da yake magana da DCL Hausa, Buba Galadima, ya yi ikirarin faɗuwar farashin, ba abin farin ciki ba ne ga mutanen Arewa, inda ya ƙara da cewa Tinubu yana son karya arewa ne ta hanyar shigo da abinci daga amfanin gona.
Ya bayyana dalilin da ya sa farashin kayan abinci ya kasance saboda gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaba Tinubu ta buɗe kan iyaka domin shigo da abinci da yawa musamman shinkafar ƙasashen waje, tare da kawo cikas ga ‘yan kasuwa.
“Dalilin da ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi saboda rashin tsaro da manoma ba sa iya zuwa gona don gudanar da ayyukansu. To, ta yaya farashin ke sauka yayin da manoma ba za su iya yin noma ba? Ko da sun je gona, ina tarakta, da taki, da sauran su da za su kawo girbi mai yawa don manoma su sayar?
“Gwamnati ta fara shigo da abinci da yawa, kuma hakan zai sa tattalin arzikin Arewa, wanda ya dogara da noma ya ragu, saboda da yawa ba za su iya noma don samun riba mai ma’ana ba,” inji shi.