Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin jirgin sojin sama mai ƙirar 401 ya faru don jajenta wa dangin mutane biyun da suka rasa rayukansu.

Jirgin dai ya faɗo ne a Kaduna da yammacin Talata a wani sansanin sojan sama a Kaduna.

a lokacin da ya ziyarci Kaduna ranar Larabar da ta gabata don jajenta wa iyalai, abokai da ‘yan uwan matuƙa jirgin saman da ya faɗo a Kaduna mai ƙirar 401 na makarantar koyon tuƙin jirgi, inda ya tabbatar da cewa an ɗauki dukkan matakan da suka dace don kauce wa sake afkuwar hakan a nan gaba.

Jami’in Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na rundunar, Edward Gabkwet, Air Commodore ne ya bayyana wa manema labarai hakan ranar Laraba a Abuja.

Rundunar ta kuma bayyana sunan dakarun da haɗarin ya rutsa da su da suna Laftanal Abubakar Muhammed Alkali da Laftanal Elijah Haruna Karatu.

Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya ce za su yi ‘nutsattsen bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin’.

Kazalika, Amao ya tabbatar wa jami’an rundunar maza da mata na makarantar koyon tuƙin jirgin sama ta 401 da cewa za su ɗauki dukkan matakan kariya da suka dace na daƙile aukuwar irin wannan hatsari a gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *