Daga BASHIR ISAH
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bai amince da wani ƙarin albashi ga zaɓaɓɓun ‘yan siyasa da ma’aikatan fannin shari’a ba kamar yadda rahotanni suka nuna.
Mai magana da yawun Tinubu, Dele Alake, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
Alake ya bayyana haka ne a matsayin martani ga rahoton da aka yaɗa kan cewa Shugaban Ƙasar ya amince da ƙarin albashi da kashi 114 wa kansa da mataimakinsa, gwamnoni da ma ma’aikata a ɓangaren shari’a.
Tun farko, an ga rahoton da ya ce Hukumar Tarawa da Raba Kuɗin Shiga ta Ƙasa (RMAFC), ta yi ƙarin albashi da kashi 114 don amfanin Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa da masu riƙe da muƙaman sisaya haɗi da ma’aikatan ɓangaren shari’a.
Lamarin da Fadar Shugaban Ƙasa ta bakin Alake ta ce hakan ba gaskiya ba ne.
“Muna bayyana cewa babu wata amincewa da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da ƙarin albashi, kuma babu wani batu mai kama da wannan da ya zo gaban Shugaban,” in Alake.