Daga BELLO A. BABAJI
Fadar Shugaban ƙasa ta dakatar da batun tantance sabbin ministoci bakwai da aka ayyana su don bai wa kowannen su damar kimtsawa.
Da farko dai an tsara gudanar da taron tantancewar ne a ranar Talata a zauren Majalisa wanda daga bisani Fadar shugaban ƙasar ta ɗage zuwa ranar Laraba.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattijai, Basheer Lado ya bayyana hakan wa manema labarai.
A ranar Larabar da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya tsige wasu ministoci biyar tare naɗa wasu goma cikin sahun waɗanda da za a bai wa muƙaman ministoci inda kuma ya miƙa sunayen wasu bakwai ga Majalisa don tabbatarwa.
Shugaba Tinubu ya bada sunan Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu a matsayin ƙaramar Ministar Harkokin Waje; Nentawe Yilwatda, Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci wanda hakan ya kawo ƙarshen Ministar da aka dakatar daga kujerar, wato Betta Edu daga muƙamin.
Sauran sun haɗa da; Maigari Dingyaɗi, Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki da Jumoke Oduwole, Ministar Masana’antu sai Idi Maiha a matsayin Ministan Ci-gaban Kiwo (wadda sabuwar Ma’aikata ce) da Yusuf Ata a matsayin ƙaramin Ministan Gine-gine da kuma Suwaiba Ahmad a matsayin ƙaramar Ministar Ilimi.