Fadar Shugaban Ƙasa ta gaskata afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame, cewar Garba Shehu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Fadar Sugaban Ƙasa ta gaskata afuwar shugabanci da aka yi wa tsoffin gwamnoni Joshua Dariye da Jolly Nyame, tana mai faɗin afuwar ta biyo bayan tanade-tanaden dake cikin kundin tsarin mulkin ƙasa ne.

Fadar ta kuma bayyana cewar, afuwar ba ta yi tsaiko ko karan-tsaye wa yaƙi da rashawa da cin hanci ba, har ila yau an zaƙulo tsofaffin gwamnonin ne da zummar yi masu afuwa bisa la’akari da yanayin lafiyar su.

Tun makon da ya gabata, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana cewar, an yi wa ‘yan Nijeriya kimanin guda 159 dake cibiyoyin gyara halaye daban-daban na ƙasar nan afuwar shugabanci, lamarin da ya haddasa wa gwamnatin Shugaba Buhari soke-soke daga ɗimbin ‘yan Nijeriya, har suma waɗanda aka yi wa afuwar basu tsira ba.

Amma kuma fadar shugaban ƙasa a cikin wata sanarwa da babban mataimaki wa Buhari akan lamuran faɗakarwa da yayatawa, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana cewar, afuwar an yi ta ne da tsarkakakkar zuciya.

Sanarwar ta zayyana kamar haka: “Fafar Shugaban Ƙasa tana son bayar da ƙarin haske akan ƙuduri da Kwamitin Bayar da Shawara Akan Afuwa na Fadar Shugaban Ƙasa ya gabatar wa Majalisar Ƙoli ta Ƙasa bisa buƙatar yin afuwa daya faro tun daga ɗaurarrun da kuma wasu majiɓanta lamarin kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar.

“Sashi na 175 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya (wanda aka yi wa gyara) ya bai wa shugaban ƙasa yin amfani da wannan ƙuduri na mulki, ‘yin afuwa ga wanda yake tsare ko majiɓancin haka bisa tanade-tanaden dokar majalisar ƙasa akan afuwa, walau ɗungurungum kona wani wa’adin doka, domin sauƙaƙawa na har Insha-Allahu kona wani taƙaitaccen lokaci bisa kowane irin horo da aka ƙaƙafawa mutum na wani zayyanan nen laifi, ko kuma share dukkan ko wani ɓangaren laifi da aka ƙaƙafawa mutum; ko musanyawa da wani sauƙaƙeƙƙen tanadi na horon da aka ƙaƙafawa mutum dangane da laifi daya aikata, ko ƙwacewa ya zuwa ga hukuma bisa tanadin wannan laifi.

“Gwamnatin Tarayya ce ta kafa kwamiti da aka ɗora masa nauyin bayar da shawarwari bisa buƙatar yin afuwa ga masu laifuka (PACPM) a ranar 28 ga watan Agusta na shekara ta 2018 da zumma ko alhakin taimaka wa shugaban ƙasa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora masa na yi wa mai laifi afuwa ko samar da sauƙi ga wanda aka yi wa hukunci bisa lamuran da suka cancanci yin hakan.

“Kwamitin ya zayyana rahoton sa a watan Maris na shekarar 2020, kana ya sake zama a ranar Alhamis 28 ga watan Satumba na shekarar data gabata – 2021 biyo bayan wasu tarin buƙatu dake neman afuwa ko sauƙaƙawar shugaban ƙasa daga wasu ‘yan Nijeriya daga sassa dabam-dabam na ƙasar nan.

“A fayyace, gabatar da wannan batu a makon da ya gabata wa majalisar ƙoli ta ƙasa da mambobin ta suka haɗa da tsoffin shugabannin qasa, tsoffin manyan alqalan shari’a na qasa, da gwamnoni ko wakilan jihohi 36 da babbar birnin tarayya ta Abuja, da kuma sauran mambobi da doka ko tsari ya fauwala, a jimlace wani gagarumin tsari ne daya samu jagorancin doka, don haka ba za a danganta shi da qoqarin cimma wata buqata ko manufa ta siyasa ba.

“Haqiqa jazamun ne batutuwan tsoffin gwamnoni guda biyu daga cikin ximbin waxanda akayi wa afuwa, zasu kawo ko hassada sharhi na siyasa, musamman a wannan lokaci da zaven gamagari na qasa ke gabato  wa, shugaban qasa yaci tura da wasu batutuwa marasa filako gareshi, kuma waxanda zasu haddasa zalunci ga ximbin jama’a, idan da zai yi burus da batutuwa da suka wajabta da aka gabatar da shawarwarin yin afuwa akan su, saboda kawai wani daga cikin su tsohon gwamna ne. Ai koda tsoofin gwamnoni akwai buƙatar yi masu adalci a cikin tanade-tanaden doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *