Fahimtar juna, ita ce tushen Ingantacciyar Dangantaka

Daga FA’IZA MUSTAPHA

A baya-bayan nan ne aka yi bikin buɗe cibiyar koyar da harshen Sinanci da kamfanin gine-gine na ƙasar Sin na CRCC ya yi wa kwaskwarima, a makarantar sakandare ta Garki Area 11 dake Abujan Nijeriya.

Haka zalika a jiya, an yi bikin buɗe kwalejin Confuscious a jami’ar Alkahira dake Masar, don ƙaddamar da shirin koyar da harshen Sinanci.

Bambancin harshe babban ƙalubale ne dake karan tsaye ga kusan kowacce mu’amala, sannan fahimtar juna, ita ce tushen ingantacciyar dangantaka da za ta tabbatar da ɗorewarta.

Muddin aka samu fahimtar juna ta fuskar al’adu da harshe, to za a samu zaman lafiya da ci gaba tsakanin ɓangarori daban daban.

A nan gaba, cikin shekaru ƙalilan, al’ummomin Sin da Afrika za su dunƙule.

Shirye-shiryen na koyar da harshen Sinanci a Nijeriya da Masar, sun shafi makarantu ne na sakandare, wannan kuma ya nuna kaifin basirar Sin na mayar da hankali kan yara manyan gobe.

Kamar yadda ake cewa, da zafi-zafi a kan daki ƙarfe, wato fahimtar al’adun Sin da ma harshen Sinanci ga yara a nahiyar Afrika, za ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina al’ummar Sin da Afrika ta bai ɗaya, kuma mai kyakkyawar makoma.

Wasu za su ce, to shin ita ƙasar Sin tana koyar da harsunan Afrika a ƙasarta?

Abun burgewa shi ne, ƙasar ta shafe gomman shekaru tana koyar da harsunan Afrika, har ɗalibai na samu shaidar digiri a harshen Hausa da sauran wasu harsunan Afrika kamar Kiswahili.

Baya ga haka, da idona, na ga wani littafin karatu na daliban ajin firamare, dake ɗauke da harshen Hausa.

A sannan nan ƙara fahimtar lallai Sin ta yi nisa a ƙoƙarinta na haɓaka dangantaka da Nijeriya da ma sauran ƙasashen Afrika.

Ilimi shi ne gishirin rayuwa. Haka kuma ƙashin bayan ci gaban kowacce al’umma.

Yadda gwamnati da kamfanonin ƙasar Sin ke mayar da hankali wajen bayar da gudunmawa ga kyautatuwar ilimi a Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika, ya cancanci yabo, domin lamari ne da za a ga alfanunsa a nan gaba.

Kamar yadda shugaban hukumar ilimi a matakin farko ta birnin Abuja, Alhassan Sule ya bayyana, daɗaɗɗiyar dangantakar Sin da Nijeriya ta taimaka sosai ga aikin samar da ilimi a ƙasar.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha