Falasɗinawa za su yi farin ciki da inda za mu kai su – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada aniyarsa ta karɓe Gaza da kuma kwashe Falasɗinawan da ke wurin zuwa ƙasashen Jordan da Masar tare da wasu ƙasashen Larabawa.

Yayin ganawa da Sarki Abdallah na Jordan wanda ya ziyarce shi a Washington, Trump ya ce yana da yaƙinin cewar za su samu fili a ƙasashen Jordan da Masar inda za a kai Falasɗinawan da za a kwashe daga Gazar.

Shugaban ya ce bayan kammala tattaunawar da suke yi za a samu wurin da za a aje Falasɗinawan da ke Gaza da za su zauna cikin farin ciki.

Yayin tsokaci akan matsayin Trump, Sarki Abdallah wanda ya bayyana cewar ƙasarsa za ta kwashi ƙananan yara 2,000 daga Gaza zuwa Jordan, ya ƙara da cewar Masar za ta gabatar da shirin da suke da shi dangane da makomar Gazar.

Sarkin ya kuma ce akwai wani taron shugabannin ƙasashen Larabawa da Saudi Arabia za ta jagoranta wanda zai kunshi kasashen su duka domin ɗaukar matsayin bai ɗaya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewar kashi 74 na Amurkawa ba sa goyan bayan wanann shiri na Trump wanda zai raba Falasɗinawa daga Gaza.

Rahotanni sun ce ƙasashen Jordan da Masar na fargabar rasa tallafin kuɗaɗen da suka saba samu daga Amurka domin gudanar da harkokin su na yau da kullum idan suka bijirewa shirin na Trump.

Jordan na samun kuɗin tallafin da ya kai Dala biliyan 1 da miliyan 450 kowacce shekara daga Amurka, abinda ya sanya ta cikin manyan kawayen ta a yankin Gabas ta Tsakiya.

ɗaya daga cikin shugabannin Falasɗinawa Mustafa Barghouti ya bayyana Trump a matsayin wanda ya gurgunta yarjejeniyar tsagaita wutar da Isra’ila ta ƙulla da ƙungiyar Hams da kuma bada damar gudanar da kisan ƙara dangi akan Falasɗinawa. RFI