FAMWAN ta buƙaci ’ya’yanta su yi rijistar zaɓe a a Jigawa

Umar AKILU MAJERI a Dutse

An buƙaci ’ya’yan Ƙungiyar Musulmi Mata ta FAMWAN a duk inda suke a Jihar Jigawa da su yi ragitar katin zaɓe domin zaɓar shugaba na gari a zaɓen 2023.

Shugabar Mata ta Ƙungiyar, Hajiya Maimuna Ahmed Abubakar ce ta yi wannan kiran a wata ganawa da ya yi da wakilinmu na Jigawa a lokacin da ya ke zantawa da ita a Birnin Dutse da ke Jihar Jigawa.

Ta kuma buƙaci gwamnati da masu hannu wajen agazawa ƙungiyar a gyara makarantarsu da Islamiyya da suke koyarwa da matan aute da zawarawa da ta samu matsala a lokacin damina kuma makarantar ta ke buƙatar gyare-gyare.

Da ta ke bada tarihin kafuwar ƙungiyar ta FAMWAN ta ce, ƙungiyace da aka kafata domin yaɗa manufar addinin Musulunci, kuma an kafa ta kimanin shekaru talatin da suka gabata.

Ta ce, bayan kafa ƙungiyar, ‘ya’yan ƙungiyar sun fuskanci ƙalubale masu yawa kasancewar wadda ta kawo ƙungiyar a Nijeriya wata Baturiyace matar wani malami alƙali a Nijeriya da ake cewa Lemu, inda wasu suke wa ƙungiyar mummunar fasara da cewar wata ƙungiyace da zata farraƙa kan ma’aurata.

Hajiya Maimuna ta ce, yanzu ƙungiyar sai san barka domin al’amuranta suna tafiya aidai saboda al’umma da dama sun fahimci manufarta.