Fantsamar fursunoni cikin jama’a babban haɗari ne ga tsaron ƙasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ‘yan watannin baya-bayan nan labarin kai hari da ɓalle gidajen kurkuku, domin fitar da fursunoni, na neman zama gama gari, sakamakon yadda ake yawan samun aukuwar irin wannan ɗanyen aiki a sassan ƙasar nan daban-daban.

A cikin shekarar nan ta 2021 kaɗai rahotanni sun bayyana cewa, fursunoni da ake zargi da aikata laifuka iri daban-daban har fiye da kimanin 2,500 ne suka tsere daga gidajen yari ko cibiyoyin Gyara Halinka da ke sassan ƙasar nan. Daga watan Afrilu zuwa Nuwamba, gungun ɓata gari ne suka far wa Cibiyar Gyara Halinka da ke jihar Imo inda suka fitar da fursunoni aqalla 1,800, haka ma a Kabba da ke jihar Kogi fursunoni kimanin 240 ne suka gudu daga inda ake tsare da su daga cikin fursunoni 294, sai kuma na baya bayan nan a Jos da ke jihar Filato fursunoni 252 ake farautar su yanzu haka ba a san inda suka shiga ba.

Kusan a duk inda ake irin wannan fashe fashen gidajen kurkuku fursunoni ƙalilan ne ake samun rahoton an sake cafko su a wata mavoya ko daga wasu rahotannin sirri, ko kuma su koma bisa raɗin kansu. Kamar a Jos inda aka ce an sake mayar da fursunoni 10 ban da waɗancan na baya da ake nema, yayin da wasu iyaye suka mayar da yaran su 2 da suka koma gida. Amma sauran da suke guduwa cikin jama’a suke komawa su vuya, ko kuma su koma cigaba da aikata laifukan da suke yi. 

Fasa kurkuku da fitar da fursunonin da kotu ta ba da damar tsare su, babban laifi ne a dokar ƙasa, saboda tamkar kai hari ne kan gwamnati, domin kuwa Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida, hukuma ce da aiki da ƙarfin doka. Don haka fasa katanga ko ƙofofin shiga kurkuku babban laifi ne, ba ma a Nijeriya kaɗai ba haka abin yake a kowacce ƙasa ta duniya. 

Ko da ya ke ƙungiyoyin da suke aikata wannan ta’asa, ba su da wata alaƙa da juna, ƙungiyoyi ne dai na ‘yan ta’adda da ke ɗaukar makamai suna aikata manyan laifuka da suka shafi fashi da makami, ayyukan tsageranci, masu tada ƙayar baya, Boko Haram da dai sauran su. Amma salon yadda suke aiwatar da hare haren nasu kusan iri ɗaya, sau da dama za ka ji a rahotanni cewa, wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai hari wani gidan yari, sun buɗe wuta sun valla ƙofofin shiga da sanya wuta a sassan gine-gine gidan ko kuma su rusa wani sashi na ginin katangar, ta hanyar amfani da sinadarai masu fashewa, da lalata ofisoshi da kayan aiki. 

Wani babban abin takaici da yake ɗaga hankalin ‘yan ƙasa shi ne, irin yadda maharan da ke tafiya cikin gungu kan iya kai hari har kuma su samu nasarar aiwatar da manufar su ta kuɓutar da waɗanda suka je nema, su koma inda suka fito ba tare da fuskantar wata turjiya mai zafi ba. Ko da yake ba za a ce jami’an tsaro ba sa aikin su na tsare gidajen yari ko kare rayukan jama’a ba, amma a mafi akasarin lokuta ana zargin sukan nemi mafaka ne su ma saboda tsoron rayuwar su, sakamakon yadda maharan ke zuwa da manyan makaman da suka fi nasu, suka suke ɓarin wuta ba ji ba gani. Sai daga baya idan ƙura ta lafa za su bi baya da harbe harbe ko farautar waɗanda suka tarwatse, don mayar da su. Sauran bayanin kuma ya zama turanci da rubuce-rubuce. 

Bincike ya nunar da cewa, a gidajen yari 240 da ake da su a sassan ƙasar nan akwai fursunoni fiye da 70,000, waɗanda a cikin su kashi 27 cikin ɗari ne kacal wato kimanin fursunoni 20,000 aka zartarwa hukunci, yayin da mafi akasari ke zaman jiran shari’a. Akasarin su suna rayuwa ne a ƙuntace cikin wani muhalli marar tsari da tsafta. Su kansu jami’an da ke tsaron gidajen kurkuku a mafi yawan Cibiyoyin Gyara Halinka da ake da su a ƙasar nan, ba sa samun kulawar da ta dace, bayan ƙarancin da suke da shi, ga kuma rashin ingantattun makamai, ga rashin kuɗaɗen gudanarwa da rashin kayan aiki na zamani. An ce a wasu gidajen yarin ma babu na’urar ɗaukar hoton sirri ta CCTV da ake buƙata, a inda akwai ma ba sa aiki. 

Wani babban haɗarin kuma shi ne fantsamar waɗannan manyan masu aikata laifuka cikin jama’a, domin kuwa da yawan su za su koma ne su cigaba da aikata halayen da suka saba, hakan kuma shi ne zai haddasa yawaitar aikata laifuka da cigaba da taɓarɓarewar tsaro. Sannan har wa yau barazana ce ga rayuwar jami’an tsaro da ke kula da gidajen yari ko gabatar da waɗanda ake zargi a gaban kotu. Kamar yadda rahotanni suka nuna a lokacin harin da aka kai gidan yarin Oko a jihar Edo a shekarar da ta gabata, lokacin zanga zangar ENDSARS inda fursunoni da dama suka fantsama gari, har aka yi zargin wani daga cikin su ya bi dare ya je ya kashe ɗan sandan da ya shigar da ƙarar sa gaban kotu. 

Ya kamata hukumomin kula da tsaron cibiyoyin Gyara Halinka na ƙasa su zauna su fitar da wani sabon tsari na kula da tsaron fursunonin nan, tattara bayanan su a na’ura mai ƙwaƙwalwa, don sake gano bayanan su ko da kuwa an lalata waɗanda ke ajiye a kurkukun da suka gudu. Daga ɓangaren tsaro lallai ne a samar da na’urorin zamani da sabbin dabaru irin na sauran ƙasashen duniya, don kawo ƙarshen wannan abin kunya da ke neman zama ruwan dare. 

Da fatan ƙalubalen da aka ambata a sama gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki za su duba, su ɗauki matakin da ya dace, don haka ne zai taimaka wajen rage nauyin da ke kansu na samar da tsaron ƙasa da rayukan al’umma. Sannan wajibi ne a samar da kwamiti na wasu amintattu da za su gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan jami’an da ke aiki a irin waɗannan gidajen yari da ake samun rahotannin kai hari, saboda zarge-zargen da suka yi yawa, inda ake ganin irin wannan abu ba ya yiwuwa sai da haɗin bakin ‘yan gida. Kamar misalin abin da ya faru a babban kurkukun Jos. 

Lallai Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka ta ƙasa ta yi bincike sosai don ta tsaftace baragurbi daga cikin jami’an ta, waɗanda ta iya yiwuwa da su ake amfani wannan mummunan aiki ya samu nasara. 

Allah ya kawo mana ƙarshen wannan musiba ta rashin tsaro da ta’addanci a qasa, ya kuma bai wa shugabannin mu kishi, hikima da dabarar ɗaukar ingantattun matakan kawo ƙarshen irin wannan mummunan aiki. Amin.