Faransa ta sha alwashin kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa matasa

Gwamnatin Faransa na duba yuwuwar yadda za a kawo ƙarshen hare-haren da ke faruwa a tsakanin matasa, bayan cakawa wani ɗan shekara 15 wuƙa da wani matashi ya yi a ƙarshen mako, ɗaya daga cikin jerin hare-haren da ya girgiza al’ummar ƙasar.

Firaministan Faransa Gabriel Attal ya shirya tarurrukan da jam’iyyun siyasa kan yadda za a tunkari wannan matsala da ke neman wuce gona da iri.

Ƙasar Faransa dai ta fuskanci jerin hare-hare kan matasa daga takwarorinsu a ‘yan makonnin nan, inda masu tsatsauran ra’ayi da masu ra’ayin mazan jiya suka danganta wannan matsala da manufofin gwamnati na sassauta sha’anin shige da fice.

A harin baya-bayan nan, an kashe wani matashi ɗan shekara 15 a wani artabu da aka yi a garin Chateauroux da ke tsakiyar Ƙasar Faransa ranar Asabar.

Ko da yake an tsare matashin tare da mahaifiyarsa mai shekaru 37, inda za a gurfanar da su gaban kotu nan da ‘yan kwanaki.

Masu gabatar da qara na zargin mahaifiyar matashin da ya aikata ɗanyen aiki da hannu a ciki.

A farkon wannan watan, firaminista Attal, ya ba da sanarwar ɗaukar wasu matakai na murƙushe tashe-tashen hankulan matasa a makarantu.