Farashin Shinkafa zai sakko nan da 14 ga watan Disamba

Alamu sun nuna, kungiyar manoman shinkafa da hadin guiwar babban banki Najeriya, zata karya farashin shinkafa, daga Naira 30,000 zuwa Naira 19,000 daga ranar 14 ga watan Disamba na wannan shekara.

An dau wannan mataki ne, saboda fahimtar da hukumomi da shugabannin kungiyar manoman suka yi, na cewa, wasu manyan yan kasuwa sun boye shinkafar ne da gangan, domin su sayar in tayi tsada, su ci kazamar riba.

wannan sanarwa dai ta fito ne, daga kungiyar manoman shinkafar ta IRFAN.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*