Farfaɗo da Tabkin Chadi zai taimaka wajen hana matasa ƙetarawa ƙetare – Buhari

Daga BASHIR ISAH


Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce farfaɗo da yankin Tabkin Chadi zai taimaka wajen sassauta matsalar neman ƙetarawa zuwa Turai da matasa kan yi ta hanyar ketawa ta sahara.

Buhari ya bayyana haka ne sa’ilin da ya karɓi baƙuncin takwaransa na Chadi,  Marshal Idris Deby a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Asabar.

A cewar Buhari, kimanin mutane milyan 30 ne matsalar tsukewar Tabkin Chadi ta shafa wanda a yanzu kashi 10 cikin 100 na girman tabkin ne ya yi saura idan aka kwatanta da asalin girmansa, inji sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, ya sanya wa hannu.


Buhari ya ce ya zama tilas a ja ruwa daga Tabkin Congo zuwa Tabkin Chadi domin dawo da harkoki kamar yadda suke a can baya.

Yana mai cewa idan hakan ya samu, harkokin kamun kifi da noman rani da kiwo za su dawo wanda hakan zai taimaka wajen daƙile matsalar yawa-yawan tafiya ƙasashen waje da matasa kan yi ta hanyar keta sahara da koguna suna jefa rayukansu cikin haɗari don neman cim ma burinsu na tafiya Tutai neman arziki.

A cewar Buhari, “Ina tuntuɓar masu ruwa da tsaki a Afirka da kewaye a kan yadda za a yi a farfaɗo da Tabkin Chadi.  Nijeriya ce za ta fi cin ribar abin amma kuma kowa zai amfana.”

A nasa ɓangaren, Shugaba Deby ya bai wa Buhari shawara kan ya shirya wani taro na ƙasa da ƙasa inda zai nemi a tallafa wa ƙudirinsa na neman farfaɗo da tabkin.

Buhari ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa baƙon nasa dangane da ƙoƙarin da yake yi wajen yaƙi da matsalar tsaro a yankin tabkin, musamman ma abin da ya shafi Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *