Farfagandar ƙyamar ƙasar Sin ba za ta yi kasuwa a tsibiran yankin Pacific ba

Daga CMG HAUSA

A kwanan nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Amurka ya bayyana cewa, fadar White House ta Amurka ta shirya tura tawagar musamman ƙarƙashin jagorancin Mr. Kurt Campbell, jagoran tsare tsare na ayyukan da suka shafi yankunan tekun Indiya da Pacific a majalissar tsaron ƙasa, zuwa tsibiran dake yankin, ciki har da tsibirin Solomon.

Kakakin ya ce tawagar Amurka na sa ran tattauna batutuwa da dama, ciki har da wadanda suka jibanci ƙasar Sin yayin wannan ziyara.

A baya bayan nan, Sin da tsibirin Solomon sun sanya hannu, kan yarjejeniyar cudanya a hukumance, don gane da haɗin gwiwar tsaro, sun kuma amince su hada hannu wajen tabbatar da doka da oda, da kare rayukan al’umma da duniyoyin su, da ba da agajin jin kai, da aiwatar da matakan ceto yayin aukuwar bala’u, da sauran fannoni, ƙarƙashin tsari na daidaito da cimma moriyar juna. Wannan haɗin gwiwa ya yi daidai da dokokin ƙasa da ƙasa, da kuma tsarin cuɗanyar sassa, kuma ba a yi shi domin nuna yatsa ga wata ƙasa ko yanki ba.

Ko shakka babu, ƙasashen yankin Pacific, ba ‘yan koren wani ɓangare ba ne, balle a yi amfani da su wajen rarraba kan wasu sassa, ko fito na fito da wani ɓangare. Maimakon haka, tsibirai ne dake da fatan faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙasashen waje, suna kuma da ikon zaɓar abokan hulɗa bisa radin kan su.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *