Farfesa Alkali ya ajiye muƙaminsa na shugaban Jam’iyyar NNPP

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Farfesa Rufai Alkali, ya yi murabus daga muƙaminsa a matsayin shugaban jam’iyyar.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar Alkali ya miƙa wasiƙar ajiye muƙamin nasa ne ga Sakataren jam’iyyar da nufin bai wa sabbin hannu shigowa don ɗorawa daga nasarorin da suka samu cikin taƙaitaccen lokacin da ya yi riƙe da jam’iyyar.

Ya ce, ”Ina mai sanar da kai zan ajiye muƙamina a matsayin Shugaban Jam’iyyar NNPP na Ƙasa sannan in koma gefe daga ranar Juma’a, 31 ga Maris, 2023.

“Bisa la’akari da yadda harkoki suka gudana kafin da bayan babban zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, 2023, ina da ƙwarin gwiwar jam’iyyarmu ta NNPP na da daman zama jam’iyyar da ke kan gaba da ma zarafin lashe zaɓen shugaban ƙasa ya zuwa 2027.

“Domin cimma wannan kuwa, tilas mu fara shiri da tsari a kan lokaci, kuma yanzu ne wannan lokacin,” in ji Alkali.

Ya ƙara da cewa, jam’iyyarsu na buƙatar samar da ingantattun tsare-tsare domin ba ta damar shigewa gaban sauran jam’iyyun da suke kundin Hukumar Zaɓe, INEC.

An aika da kwafin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata Alhamis, 31 ga Maris, 2023 zuwa ga mu’assasin jam’iyyar kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso; Shugaban Kwamitin Amintattu, Boniface Aniebonam da sauransu.