Farfesan Ganduje: An yanka ta tashi

A kwanakin baya ne, daya daga cikin kakakin gwamnatin Kano, Malam Abba Anwar ya sanar da manema labarai ce war, wata jami’a da ake kira Jami’ar East Carolina ta baiwa gwamna Ganduje na jihar Kano, mukamin farfesa a wasu tsangayu biyu na jami’ar, wadanda suka hada da na harkokin kasuwanci da kuma na fasahar zamani. To amma da alamu an yanka ta tashi, domin shaidu na nuna ce wa, wannan zance ba haka yake ba, kila dai anyiwa gwamnatin ta Kano papalolo ne kawai.

Wata wasika da jaridar Manhaja ta samu daga jami’ar, ta nuna ce wa wannan zance dai, zancen bur ne in ji tusa.

Wasikar da shugaban makarantar na wucin gadi Dakta B Grant ya sanya wa hannu, ta ce “Na samu sanarwar ce wa, wani mutum da ke ikirarin jami’i ne na daya daga cikin tsangayun mu, ya aika ma da wasikar daukan aiki a matsayin farfesa, wacce ke dauke da kwanan wata na ranar 30 ga watan Nuwamba, 2020. Ina so in sanar da kai ce wa, wannan wasika da ka karba mai dauke da sa hannun Dakta Victor Mbarika, na an dauke ka aiki a kwalejin fasahar sadarwa da cinikayya a matsayin farfesa ba haka bane”,

Wasikar ta kara da ce wa, a dokar wannan jami’a, shugaban jami’a ne kawai, ko ni, ko kamfanin da mu ka baiwa kwangilar daukar maaikata, ke da damar daukar wani mutum aiki a kowanne sashi na jami’ar nan. Muna sanar da kai cewa, Dakta Victor Mbarika, ba shi da wannan mukami”

“A takaice dai ina sanar da kai, babu wannan magana, kuma jami’ar mu bata dauki wani ma’aikaci ba a yanzu” in ji shugaban jamiar.

Wasikar da aka aiko a ranar 4 ga watan Disamba ta wannan shekarar, an kuma aike da kofinta ga shugabannin tsangayun biyu da abin ya shafa.

Wannan abu dai a yanzu haka, ya janyo cecekuce a tsakanin magoya baya a shafukan sadarwa na zamani da ke intanet, tun bayan da aka samu wannan sahihiyar wasika daga jami’ar. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta ce komai ba akan wannan abun takaici.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*