Faruk Lawan: Ina aka kwana kan babban batun?

A tsakiyar makon nan ne wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke wa fitaccen tsohon ɗan Majalisar Wakilai na Tarayyar Nijeriya, Hon. Faruk Lawan, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bayan da ta ce kama shi da laifin amsar na goro daga hannun wani babban attajiri kuma ƙasurgumin ɗan kasuwa a ƙasar, wato Mista Femi Otedola a shekara ta 2012 lokacin da Lawan ]in ke shugabantar Kwamitin Bincike kan Badaƙalar Tallafin Man Fetur.

A yayin da ta ke yanke hukuncin, alaƙalin kotun, Mai Shari’a Angela Otaluka, ta ce, Hon. Lawan ya kasa tabbatar wa da kotu iƙirarinsa na cewa, ya amshi kuɗin ne daga hannun Mista Otedola, domin ya samu shaidar da ta ke nuna cewa, ƙasurgumin ɗan kasuwar yana ƙoƙorin hana kwamitin gudanar da aikinsa ta hanyar ba shi cin hanci, to amma ɗan majalisar ya gaza kai rahoton hakan ga jami’an tsaro, wata hukuma da ta dace ko kuma sauran mambobin kwamitin, inda shi kuma Otedola ya yi gaggawa ya riga shi kai rahoton amsar cin hancin ga jami’an tsaro. Wannan shine ƙashin bayan musabbabin abin da Mai Shari’a Otaluka ta dogara da shi wajen yanke wa Faruk Lawan hukuncin ɗauri.

To, sai dai kuma, an shafe shekaru 11 ana tafka wannan shari’a, inda har sauye-sauyen kotu da alƙalai an yi a shari’ar, saboda zarge-zargen ƙoƙarin ƙin yi wa ]an majalisar adalci a yayin gudanar da shari’ar, wanda hakan ke nuni da cewa, lallai akwai abin dubawa. Amma babban abin dubawa a cikin batun nan shine ainihin maƙasudin abin da ya janyo lamarin shi kansa, wato bincike kan zargin badaƙalar cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci a harkokin bayar da tallafin mai da aka daɗe ana yi a Nijeriya, wanda hakan ne ya janyo har Majalisar Wakilai ta wancan lokaci ta ga wajabtar kafa kwamitin, don bincikar badaƙalar.

Rahoton kwamitin na Lawan ya gano zargin badaƙalar satar kuɗi da yi wa al’ummar Nijeriya harambe da almundahanar aƙalla Naira Tiriliyan 2.6. wato ninkin baninkin kuɗin da ake zargin Faruk Lawan da karɓa a matsayin cin hanci, don ya cire sunan kamfanin Otedola mai Zenon Oil and Gas daga jerin sunayen kamfanonin da ake zargin sun zambaci Nijeriya da ’yan Nijeriya waɗancan ma}udan kuɗi. Zargin ya shafi manyan kamfanonin harkokin mai, wa]anda Nijeriya ta ba su amanar shigo da mai, amma suka zauna akan kuɗaɗen ba tare da sun yi komai a kai ba.

Kuɗin da aka zargi Lawan da amsa a matsayin cin hanci Dala 500,000, wato daidai a Naira miliyan 96 a lokacin da aka karɓe su, duk da dai a yanzu Dala ta ƙara tashi, ta fi hakan. Amma Naira tiliyan 2.6 ba ƙaramin kuɗi ba ne da suka cancanci a kawar da kansu akai, a mayar da hankali kan kuɗin da ba su kai komai ba.

A nan ba mu na so mu ce, Faruk Lawan ya yi daidai ba ko kuma amsar cin hanci abu ne mai kyau ba, a’a, mu na so mu ce ne, bi kamata a ƙyale waccan satar zambar a bar ta ta sha ruwa ba, saboda samun shugaban kwamitin bincike da karɓar cin hanci. Hakan ya na nuna cewa, zargin da wasu ke yi na cewa, an yi wa Lawan waccan gadar zare ne, saboda ya matsa wa ɓangaren zartarwa na wancan lokaci a ƙarƙarshin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, wacce aka yi ta zargi da aikata irin waɗannan aika-aika na zargin satar kuɗi tare da shirya tuggu ga duk wanda ya nemi ya ɗaga wa gwamnatin kara.

A fili ta ke cewa, za a iya kallon Lawan a matsayin wanda ke jagorantar yaƙi aikata ta’annati a gwamnatin Jonathan da ma gwamnatocin da suka gabace shi. Don haka a abin mamaki ba ne idan aka shirya masa wata gadar zare ba, inda shi kuma ya yi mummunan kuskuren ruftawa a ciki. Don haka a lokacin da gwamnatin Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta shigo a 2015, an yi tsammanin za ta duba rahoton wancan kwamiti da ma sauran wasu kwamitoci, waɗanda a lokacin yaƙin neman zaɓe Shugaba Buhari ya yi al}awarin zai karka]e su, don aiwatar da gamsassun bayanan da ke cikinsu. To, amma tun daga shekara ta 2015 zuwa yanzu ]in ba a ga gwamnatin ta APC ta yi wani huɓɓasa wajen ɗauko ire-iren waɗannan rahotanni, don ɗaukar matakan da suka dace a kai ba.

Tabbas abin damuwa ne }warai da gaske kasancewar a samu fitattun mutane irin su Hon. Faruk Lawan da samun aikata rashawa, amma ƙin yin kataɓus da nuna halin ko-in-kula kan irin waɗancan rahotannin bincike, abu ne da ke nuni da cewa, akwai shakku kan yadda ake tunkarar batun ya}i da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Tilas idan ana so a kawo ƙarshen wannan matsala ta cin hanci da rashawa, wacce ita ummul’aba’isin kassara mafi rinjayen al’amuran ƙasar ta kowacce fuska. Idan za a iya tunawa, tun lokacin da aka fara shari’ar Faruk Lawan, an tuhume su tare da Magatakardan Kwamitin, amma sai aka wanke shi kuma masu gabatar da ƙara suka dawo suka saka shi a cikin shaidun da za su ƙalubalanci Lawan ɗin. Shi ma wannan mataki ya sanya shakku cikin batun, musamman da aka ƙi yarda a ɗauko ainihin rahoton, don aiwatar da shi.

Don haka a nan, ’yan Nijeriya su na da haƙƙin buƙatar gwamnati ta karkaɗe rahoton rahoton Lawan, ta bibiye shi, ta gano ainihin gaskiyar da ke cikinsa, don ɗaukar matakan da suka dace. Tabbas bai dace a bar maganar nan ta sha ruwa ba, domin ita ce muhimmin batun da aka fi buƙata a ƙasar!