Fasaha da kimiyyar noma na ƙasar Sin na amfanawa ƙasashen Afrika

Daga MINA

Abokai, gobe ran 23 ga watan nan, ranar samun girbi mai armashi ce ga manoman ƙasar Sin. Samun girbi mai armashi abin farin ciki ne ga manoma, amma abin da ya fi faranta musu rai shi ne taimaka wa abokansu masu buƙata wajen samun girbi mai armashi. To, a yau “Duniya a zanen MINA” na bayani ne game da yadda Sin da Afrika suke haɗin kai a fannin aikin gona.

Sanin kowa ne cewa, Sin ƙasa ce da take da al’umma mafi yawa a duniya, inda yawansu ya kai kashi 20% na al’ummar duniya baki ɗaya.

Amma, faɗin gonakinta bai wuce kashi 9% na duniya baki ɗaya ba.

Duk da haka, ta hanyar amfani da fasahohi da kimiyyar noma na zamani da ƙoƙarin da manoma ke yi, Sin ta ciyar da al’ummarta, baya ga haka tana tabbatar da cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, za ta cimma burin samar da kaso 88 cikin 100 na hatsi da al’ummarta ke buƙata.

Sinawa waɗanda a baya suka yi fama da yunwa, sun san muhimmancin hatsi matuƙa, hakan ya sa, ƙasar Sin take son taimaka wa abokanta na ƙasashen Afrika waɗanda suke ƙoƙarin tasowa.

A makon da ya gabata, kwamitin tsakanin gwamnatocin Sin da Najeriya reshen kula da haɗin gwiwar aikin noma ya gudanar da taro karo na farko ta kafar bidiyo.

Daga baya, kamfanonin Sin dake ƙasar sun yi bikin yayata shirin taimakawa ƙasashen yammacin nahiyar Afrika kafa tsarin shuka shinkafa mai inganci a birnin Abuja, jami’an masu nasaba da aikin noma da wasu ƙwararru da manoma da yawa na ƙasar ta Nijeriya sun halarci taron.

Bayanai na cewa, a shekarar 2017, gwamnatin Najeriya ta amince da wani nau’in shinkafa da kamfanin Sin ya yi nazari kuma ya gabatar, wanda ya fi ainihin iri na aka nomawa a wurin samar da ‘ya’ya da yawansa ya kai 25%.

Abin da ya samu karɓuwa matuƙa a kasuwar ƙasar.

Ban da Najeriya, Sin ta kan haɗa kai da sauran ƙasashen Afrika don ba da taimako a wannan fanni, ciki hadda Burundi da Ruwanda da Zimbabwe da Uganda da Kenya da sauransu.

A yayin da manoma suka samu amfani gona yadda ya kamata, mu kan ga murmushi a fuskokinsu.

Yanzu irin wannan murmushi na bayyana a fuskokin nanoma na ƙasashen Afrika sakamakon haɗin kai tsakanin Sin da Afrika a wannan fanni.

Sinawa na da wani karin magana cewa, Ka so wa dan uwanka abin da ka so wa kanka.

A ko da yaushe Sinawa, na more fasahohi da kimiyya masu kyau da abokansu, don samun ci gaba tare.