Fasalin Naira: ‘Yan siyasa da bankuna suka haddasa ruɗani, inji ‘yan kasuwa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Watanni uku da Gwamnatin Tarayayr Nijeriya ko kuma Babban Bankin Ƙasa ya bayar a matsayin lokacin ƙarshen wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200 da 500 da kuma Naira 1000 da aka canja wa launi zai cika ranar Talata mai zuwa, wacce ta yi daidai da 31 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2023 ya haifar da ruɗani a wajen al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi wanda yanzu haka ya sanya waɗansu ‘yan kasuwa rufe shaguna da kuma daina waɗansu sana’o’i saboda kaucewa makarowa da kuɗaɗen a hannu zuwa ranar ƙarshe.

Waɗansu ‘yan kasuwa da yaran ‘yan siyasa a jihar Kebbi kakarsu ce ta yanke saƙa saboda a  hannunsu ne kawai ake iya samun sababbin kuɗi a halin yanzu, kuma sun mayar da abin sana’a inda suke karɓar Naira dubu ɗaya a dubu goma idan za su musanya sababbin kuɗi da tsofaffi saboda suna da galihun samun sababbin ku dai daga bankuna yayin da a bankuna layi ya yi yawa, har ya kai ga waɗansu tun ƙarfe huɗu zuwa biyar na asuba suke soma zuwa su shiga layi kafin gari ya waye, yayin da a waɗansu bankuna kuma lamba ake bai wa mutane su jira har sai lokacin kiran lambar su ya yi idan kuma a ranar kiran bai kai mutum ba sai ya tafi gida sai gobe, inda waɗansu kuma ‘ya’yansu ko kuma su ɗauki hayar waɗansu yara su shiga musu layi a bankuna.

Malam Muhammadu Aminu Sani wani magidanci ne da ya bayyana cewa shi kam a wajen sa gwamnatin Nijeriya ba da gaske ta ke yi ba ko kuma ba ta shirya wa maganar canjin ba, idan kuma da gaske ta ke yi to ba shakka bankuna sun yi mata kutunguila saboda yau 25 ga watan Janairu 2023 saura kwanaki shida wa’adin canjin kuɗin ya cika, amma ba ka ga ana hada-hada da sababbin takardun kuɗin ba, hasali ma kwata-kwata bai fi sati biyu ba da aka soma ganin ɗaiɗaikun takardun sababbin kuɗin nan ba hannun talakawa ba. 

“Yanzu haka duk wanda ya tafi banki ba za a ba shi sababbin kuɗin ba sai dai tsofaffi idan ya shiga layin akwatunan ATM ba, wannan shi ne ya sanya a ke ganin ba ta shirya canja kuɗin ba idan kuma da gaske ta buga sababbin kuɗin ta rarrabawa shi kam talaka bai gan su ba, saboda har yanzu ba wani waje da za ka je ka ga ana cinikayya da sababbin takardun kuɗin sai dai hannun yaran ‘yan siyasa da kuma masu wata alaƙa da banki, amma ba dai hannun talakawa ba.”

Ya ƙara da cewa ranar Laraba ya tafi ATM tun safe tare da yaronsa aka ba shi lamba ta 138 amma har zuwa ƙarfe biyar na yamma bai kai ga samun kuɗi ba har mutane suka fusata suka wargaza layin.

Ba shakka ana cikin wahalar da ya ke ganin waɗannan kwanaki shida da suka rage ba za  su isa a canja kuɗaɗen da ke hannun mutane ba, tilas sai waɗansu da yawa sun yi asara saboda a nan garin Argungu banki ɗaya kacal ne akwai, kuma cunkoso ya yi yawa, uwa-uba babu wata cibiyar hada-hadar kuɗaɗe ta POS da za a iya samun sababbin kuɗi.

Malam Aminu Sani ya bayyana wannan a matsayin wani shiri da bankuna suka kitsa don su ne ba su saki sababbin kuɗin ba tun watanni biyu da suka wuce, sai yanzu da aski ya zo gaban goshi abin ya zama gaba zaƙi baya sayaki, saboda idan mutum ya kai kuɗi masu yawa ba za su ba shi madadin su ba, su kan ce wai babu kuɗi sai dai su nemi ya saka a asusunsa na ajiya, saboda haka ya nemi gwamnati da ta ƙalubalanci bankuna bisa ga wannan manakisar da suka shirya don ƙara matsi ga talakawa, idan da gaske ne ta rarrabawa bankuna kuɗaɗen watanni biyu ko uku da suka gabata.

Duk wanda ke da hannu a cikin wannan tsananin da al’umma ta shiga yana rokon Allah da ya bi musu haƙƙinsu saboda babu abin ɓacin rai da ya wuce mutum ya je da kuɗinsa a ce ba za a karɓa ba, wanda haka ya yi sanadiyyar kwana da yunwa a waɗansu gidaje.

A ɗaya ɓangaren Sheikh Abdulrahaman Isah Jega, Shugaban haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Shugabannin Malamai ta Jihar Kebbi a madadin ƙungiyar ya ja hankalin gwamnati da ta ji tsoron Allah ta yalwata wa’adin canjin kuɗin nan saboda al’umma suna cikin tashin hankali, inda yanzu har ta kai ga waɗansu gidajen an kasa yin abinci saboda kowa yana jin tsoron karvar tsofaffin kuɗi.

A shagunan hada-hadar kuɗaɗe na POS ba za ka samu sababbin kuɗi ba, yayin da a bankuna kuma layi ya yi yawa, uwa-uba akwai ƙananan hukumomin da ba ko bankunan ba su da kamar Augie, Dakingari Arewa da dai sauransu, sai kuma manyan garuruwa irinsu Argungu, Yawuri da Zuru duk bankuna ɗaya-ɗaya kacal su ke da wanda bisa ga ma’auni na hankali ba za su iya wadatar da al’umma ba, akwai ‘yan kasuwa a ƙauyuka da ba ba su ma’amala da banki.

Ya ƙara da cewa, “canjin kuɗin ba laifi ba ne kuma ba wanda ya isa hana gwamnati ta aiwatar amma dai wa’adin ne al’umma suka yi ƙorafi kan malamai sun ja bakunansu sun yi shiru, shi ne ya sanya haɗaɗɗiyar ƙungiyar malamai ta zauna ta ga ya kamata ta sauke nauyin da Allah ya dora mata.

Saboda haka har wa yau muna ƙara kira kira ga gwamnati da ta ji tsoron Allah ta tausayawa al’umma wanda rashin kara wa’adin canjin kudin nan yana iya haifar da kowane irin masifa ga milliyoyin mutane.” 

Wani ɗan kasuwa da da ya nemi a sakaya sunansa ya kai kuɗi sama da Naira milliyan ɗari wani banki a Kebbi ranar Larabar da ta gabata ya bayyana wa wakilinmu da cewa kwana biyu yana kan layi sanadiyyar rashin kai kuɗin banki da wuri ya ce yana da kuɗin ajiye a gida amma a tunaninsa canjin kudin ba zai tabbata ba ko kuma ana iya ƙara wa’adin, shi ya sanya shi jan ƙafa wajen kai kuɗin banki.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a Kebbi bankuna sun bayar da gudummawa wajen haddasa  wannan matsala ta cunkoso da asara da matsi ga al’umma sanadiyyar rashin saka sababbin kuɗi a cibiyoyin ɗibar kuɗi na ATM wanda shi ne ya sanya mutane suka cigaba da hada-hada da tsofaffin kuɗaɗen sai bayan aski ya zo gaban goshi suka tabbatar da ba ja da baya wajen canza ranar 31ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar ƙarshen wa’adin amfani da su.

Sai dai wani ma’aikacin banki bisa ga sharaɗin sakaya sunansa ya bayyanawa Jaridar Blueprint Manhaja da cewa maganar gaskiya ‘yan siyasa ne suka mamaye bankuna ta hanyar neman bankunansu su kai musu sababbin kuɗaɗe, saboda haka ba sababbin takardun Naira dubu da ɗari biyar da kuma ɗari biyu a bankuna sai kwanan nan.

Haka zalika waɗansu bayanai daga garuruwan da ke danganen iyakar Nijeriya da Nijar sun bayyana cewa a can babu sababbin kuɗi kuma babu tsofaffin, saboda haka sai dai su kan yi musanya wajen cinikayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *