Fashewa mai ƙarfi ta yi ajalin mutun huɗu a Kogi

Daga BASHIR ISAH

An samu aukuwar fashewa mai ƙarfi da safiyar Alhamis a yankin Okene cikin Jihar Kogi, lamarin da ya yi ajalin aƙalla mutum huɗu kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya nuna.

Majiyarmu ta ce, fashewar ta auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe na wannan rana.

An ce fashewar ta auku ne a kusa da fadar Sarkin Ibira da ke hanyar Kuroko a Okene.

Haka nan, fashewar ta yi sanadiyar ƙonewar wasu abubuwan hawa a yankin.

Wani ganau ya ce, fashewar ta auku ne a cikin wata mota da wasu babura, inda duka matuƙa baburan suka mutu nan take.

“Ina cikin gidan sa’ilin da na ji ƙarar fashewa mai ƙarfi, ko da na fito na tarar da mota da babura biyu na ci da wuta kusa da babbar ƙofa ta biyu ta shiga fadar Sarkin,” in ji ganau.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Ovye-Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ovye-Aya ya ce, ‘yan sanda na kan bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.